Buhari: Za mu kara tsanani akan yaki da rashawa daga 2019

Buhari: Za mu kara tsanani akan yaki da rashawa daga 2019

- Shugaban kasa Buhari ya sha alwashin tsananta yaki da cin hanci da rashawa bayan nasararsa a zaben 2019

- Shugaban kasar ya sha alwashin ci gaba da tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya yayin kaddamar da yakin neman zabensa a jiya cikin birnin Uyo na jihar Akwa Ibom

- Shugabannin jam'iyyar APC sun yi kira tare da gargadin haramta jam'iyyar adawa ta PDP komawa kan karagar mulkin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba bu shakka gwamnatin sa daga shekarar badi za ta kara matsanancin tsanani wajen daura damarar tare da zage dantsen ta kan yakar annobar cin hanci da rashawa da ta yiwa Najeriya katutu.

Shugaban kasar a jiya Juma'a ya sha alwashin cewa, gwamnatin sa za ta kara tsanani wajen yakar cin hanci da rashawa yayin da al'ummar kasar nan suka sake kada masa kuri'u a babban zaben kasa da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu na 2019.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Buhari ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar sa ta APC da aka gudanar cikin birni Uyo na jihar Akwa Ibom.

Shugaba Buhari yayin kaddamar da yakin neman zabe a birnin Uyo

Shugaba Buhari yayin kaddamar da yakin neman zabe a birnin Uyo
Source: UGC

Ya sha alwashin tabbatar da ci gaba da kwararar romon dimokuradiyya domin al'ummar kasar nan su sharba ba bu dare ba bu rana.

Cikin zayyana nasa jawaban, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya ce shugaba Buhari ya samu karamci a idon duniya sakamakon nagarta ta gaskiya da amana da ya kamata al'ummar kasar nan su mike tsaye wurjanjan wajen kada masa kuri'u a zaben badi.

KARANTA KUMA: Hotuna a wasu lokuta yayin rayuwar tsohon shugaban kasa, Marigayi Shagari

Kazalika babban jigo kuma Kanwa Uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce kada al'ummar Najeriya su yi kuskuren sake bai wa jam'iyyar adawa ta PDP damar hayewa karagar mulkin kasar nan duba da yadda ta durkusar da Najeriya tsawon shekaru 16 a gadon mulki.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya ce tabbas ya cika dukkanin wasu alkawurra da ya daukarwa al'ummar Najeriya yayin yakin neman zaben sa a shekarar 2015 da ta gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel