Kayi laifin da ya cancanci hukuncin kisa - Atiku ya fadawa Buhari

Kayi laifin da ya cancanci hukuncin kisa - Atiku ya fadawa Buhari

- Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku Abubakar ya mayar da martani da kalaman da mai magana da yawun kungiyar kamfen din Buhari, Festus Keyamo ya yi a kan Atiku

- Keyamu ya ce idan da hukumomin Najeriya suna aiki yadda ya dace da tuni an tura Atiku zuwa gidan yari saboda rashawa

- Shi kuma Ibe ya ce ai da hukumomin Najeriya na aiki da tuni an yankewa Buhari hukuncin kisa saboda yiwa tsohon shugaban kasa Shehu Shagari juyin mulki

Mai taimakawa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP a fanin kafafen yada labarai, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga Barrister Festus Keyamo mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Buhari a kan cewa da ya yi ya kamata Atiku ya na kurkuku saboda zargin rashawa.

Idan ba a manta ba, a ranar Laraba 26 ga watan Disambar 2018, Keyamo ya fitar da wata sanarwa inda ya ce, "Idan da ace hukumomin Najeriya suna aiki yadda ya kamata, da tuni an tura Atiku gidan yari kafin Buhari ya dare kan mulki a shekarar 2015."

Kamata ya yi a yanke wa Buhari hukuncin kisa saboda yiwa Shagari juyin mulki - Hadimin Atiku ya mayar da martani ga Keyamo
Kamata ya yi a yanke wa Buhari hukuncin kisa saboda yiwa Shagari juyin mulki - Hadimin Atiku ya mayar da martani ga Keyamo
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Da ana kan tsarin gaskiya a Najeriya da tuni kana kurkuku - Buhari ya caccaki Atiku

A martanin da ya mayarwa Keyamo, Paul Ibe ya ce idan da ace hukumomin Najeriya suna aiki, da tuni an kashe shugaba Muhammadu Buhari saboda juyin mulkin da ya yiwa gwamnatin demokuradiya na shugaba Shehu Shagari a shekarar 1983.

"Ya kamata Keyamo ya rika kulawa da irin abubuwan da ya ke fadi wurin yiwa APC kamfen. Idan da ace hukumomin Najeriya suna aiki yadda ya kamata, da tuni an yanke wa Buhari hukuncin kisa saboda hambarar da gwamnatin demokradiya a 1983," kamar yadda ya rubuta a twitter.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel