Shugaba Buhari ya yi hudubar zaman lafiya a jihar Gombe

Shugaba Buhari ya yi hudubar zaman lafiya a jihar Gombe

Mun samu cewa, a yau Juma'a, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kyakkyawar huduba ta kiran al'ummar Najeriya bisa ga turba da kuma tafarki na tabbatar da zaman lafiya kasancewar hakan na daya daga cikin ababe da za su tabbatar da ci gaban kasa.

Shugaban kasar ya yi wannan kira ne yayin bikin bude gagarumar musabakar karatun Alqur'ani na kasa karo na 33 da aka gudanar a cibiyar musulunci ta jami'ar Usman Danfodio da ke jihar Sakkwato.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Ministan Zamantakewa, Mallam Suleiman Hassan, shine ya wakilci shugaban kasa Buhari a wurin babban taron da aka gudanar a birnin Shehu.

Ministan ya yi kira kan tabbatar da zaman lafiya da kuma inganta dankon zumunta a tsakankanin al'umma domin ciyar da kasar nan zuwa gaci.

Shugaba Buhari ya yi hudubar zaman lafiya a jihar Gombe

Shugaba Buhari ya yi hudubar zaman lafiya a jihar Gombe
Source: Twitter

Ya tunatar da al'umma kan romon da za su sharba yayin neman ilimi addini da kuma na zamani, inda ya ce hakan zai yi kyakkyawan tasiri na tabbatar da zaman lafiya.

Jagoran kasar ya kuma jaddada tsayuwar dakan gwamnatin su akan wanzar da zaman lafiya domin ci gaban kasa da hakan ba zai tabbata ba matukar al'umma ba su mike tsaye ba wajen neman ilimi.

KARANTA KUMA: Mafi shaharar Labarai 10 a shekarar 2018 - Bincike

Shugaba Buhari ya kuma gargadi al'ummar Najeriya kan kasancewa bisa mafi kyawun dabi'a yayin babban zaben kasa na shekarar badi. Ya kuma nemi a kauracewa zantuttuka masu harzuka al'umma da furucin nuna kiyayya da tasirin hakan na barazana ta dakile kwararar romon dimokuradiyya.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira birnin Uyo na jihar Akwa Ibom domin kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyarsa ta APC.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel