Ni me zan je nayi ma a Amurka - Atiku ya mayar da martani a kan shigar sa Amurka

Ni me zan je nayi ma a Amurka - Atiku ya mayar da martani a kan shigar sa Amurka

Bisa dukkan alamu dai tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar People's Democratic Party, Atiku Abubakar ba zai ziyarci Amurka a cikin 'yan kwanakin nan ba.

An dade ana zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar yana fuskantar tuhumar aikata rashawa musamman daga jam'iyyun adawa.

Atiku ya kasance mataimakin shugaban kasar Najeriya a tsakanin 1999 zuwa 2010.

Ni me zan je nayi ma a Amurka - Atiku ya mayar da martani a kan shigar sa Amurka
Ni me zan je nayi ma a Amurka - Atiku ya mayar da martani a kan shigar sa Amurka
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da ana kan tsarin gaskiya a Najeriya da tuni kana kurkuku - Buhari ya caccaki Atiku

"Dama mene zanje inyi a Amurka," inji Atiku a wata hira da ya yi da VOA.

"Ana zarginsa da matarsa na hudu, Jennifer Douglas da ke zaune a Amurka da laifin karkatar da kudi fiye da $40 miliyan a cikin wani rahoton da wani kwamiti na majalisar dattawar Amurka tayi a shafi na 328.

"Ms Douglas ta taimakawa mijinta wurin shigo da kudi fiye da $40 miliyan zuwa Amurka. Cikin kudin har da a kalla $1.7 miliyan na cin hanci daga kamfanin Siemies AG da kuma wasu kamfanonin bogi da suka hada da Lets Go Ltd. Inc., Guernsey Trust Company Nigeria Ltd., da Sima Holding Ltd," kamar yadda ya ke a shafi 173 na rahoton da kwamitin Carl Levin ya jagoranta.

Duk da cewa Atiku bai ziyarci Amurka ba tun lokacin da aka zarge shi da laifi a rahoton, ya musanta cewa ya aikata wani laifi.

Ya ce yana iya zama shugaban kasar Najeriya ba tare da ya ziyarci Amurka ba.

A watan Nuwamban wannan shekarar, Shugaban yakin neman zaben Atiku, Gbenga Daniel ya ce mahukunta kasar Amurka sun ce Atiku zai samu izinin shiga kasar Amurka idan ya nema.

Amma har yanzu, ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ta ki cewa komai a kan lamarin bawa Atiku izinin shiga kasar duk da irin tambayoyin da kafafen watsa labarai ke yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel