Ababe 5 da ya kamata shugaba Buhari ya kudirta domin nasara a zaben 2019

Ababe 5 da ya kamata shugaba Buhari ya kudirta domin nasara a zaben 2019

A yayin da guguwar siyasa ta mamaye duk wani kwararo da sako na kasar nan sakamakon ci gaba da karatowar babban zabe na 2019, yau jaridar Legit.ng ta kawo muku wasu ababe da ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar domin cimma nasara.

Ababe 5 da ya kamata shugaba Buhari ya kudirta domin nasara a zaben 2019

Ababe 5 da ya kamata shugaba Buhari ya kudirta domin nasara a zaben 2019
Source: Twitter

Kafar watsa labarai ta duniya watau BBC Hausa, ke da alhakin wannan dogon nazari gami da bincike akan ababen da ya kamata shugaba Buhari ya aiwatar domin nasarar sa a zaben badi.

Shafin jaridar BBC Hausa ya wassafa wannan ababe da ya kamata shugaban ya kudirta gami da aiwatarwa kamar haka:

1. Inganta tsaro

Kamar yadda wani Farfesa a jami'ar Maiduguri ya bayyana, Umar Pate ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta inganta kwazon jami'an dukkanin hukumomin tsaro musamman dakarun soji da kuma 'yan sanda domin samun zarafin dakila ta'addancin masu mummunar ta'ada a kasar nan.

Farfesa Pate ya yi kira kan tanadar managarta kuma wadatattun kayan aiki ga hukumomin tsaro domin tunkarar mafi munin masu haddasa tarzoma a kasar nan da ba su takaita kadai a kan mayakan Boko Haram ba da kuma 'yan awaren IPOB da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Nazarin farfesan ya kirayi shugaba Buhari da kuma gwamnatin sa akin mikewa tsaye wurjanjan domin kawo karshen wannan muguwar ta'ada da ke matukar ciwa al'ummar kasa tuwo a kwarya.

2. Habaka tattalin arziki

A yayin da inganta tattalin arziki na daya daga cikin ababe uku da shugaba Buhari ya sha alwashin kai wa zuwa ga gaci yayin yakin neman zaben sa a 2015, nazarin ya koka dangane da gazawar shugaba Buhari na sharewa al'ummar Najeriya hawayenta.

Ko shakka ba bu mafi akasarin al'ummar kasar nan musamman a yankin Arewa da talauci ya yi kane-kane tamkar karfen kafa, su na ci gaba da zuba idanu domin ganin tabbatuwar wannan lamari na fidda A'i daga Rogo.

3. Ci gaba da ayyukan gwamnatin baya

Hakika nazarin ya na kuma shawartar shugaban kasa Buhari a kan ci gaba da dasa ayyuka a kan na tsohuwar gwamnatin da ta shude, domin hakan yana kyautuwa ga ci gaban kasa.

Ire-iren ayyuka da nazarin ya hikaito sun hadar da samar da ingattatun dakunan karatu a makarantu, sabunta manyan hanyoyin mota da jiragen kasa da kuma ingantattun magunguna da kayan aiki na zamani a cibiyoyin da ke fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: Hatsarin Mota ya salwantar da rayukan Mutane 2 a jihar Ogun

4. Yakar cin hanci da rashawa

Nazarin na neman shugaban kasa Buhari a kan bin diddigi wasu batutuwan cin hanci da rashawa da suka bayyana musamman akan makusanta da kuma 'yan jam'iyyar sa ta APC.

Wannan lamari na gazawar shugaba Buhari ya janyo wasu tuni suka dawo daga rakiyarsa da cewar son kai ne abin ba dagaske a ke yi ba. Nazari ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ta zuba idanu kawai kan wasu shafaffu da mai ba tare da gurfanar da su ba da ya kamata tuni a dauki mataki cikin gaggawa.

5. Zawarcin masu zabe

Shekaru fiye da uku bayan nasarar shugaban kasa Buhari a zaben 2015, ya samu dumbin magoya baya da ba bu lallai ya samu makamantansu a zaben 2019. Wannan lamari ya bayu ne sakamakon bujirowar dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar.

Hasashe na nuni da cewa, Atiku zai kawowa shugaba Buhari tangarda da ko shakka ba bu zai kwashin na sa rabon na magoya baya musamman a Arewacin Najeriya.

Nazarin na shawartar shugaba Buhari a kan ya mike tsaye wajen zawarcin magoya matukar ya na muradin cimma nasara a zaben badi ko kuma a sha sa masulla.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel