Kirsimeti: Musulumi sun ci sun sha a gidan Fasto a Kaduna, hotuna

Kirsimeti: Musulumi sun ci sun sha a gidan Fasto a Kaduna, hotuna

A yayin da mabiya addinin Kirista a fadin duniya ke murna da shagulgulan bikin Kirsimeti, mabiya addinin Islama fiye da 500 sun Fasto Yohanna Buru murna a gidansa dake jihar Kaduna.

Musuluman, da suka da maza, mata, manya, yara, masu sarautar gargajiya, da kungiyoyi, sun fito daga jihohin arewa da makobtan kasashe, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Musulumin sun ziyarci Fasto Buru ne domin dankon zumunci da zai samar da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinan biyu.

Kirsimeti: Musulumi sun ci sun sha a gidan Fasto a Kaduna, hotuna
Musulumi sun ci sun sha a gidan Fasto a Kaduna
Asali: UGC

Limami a Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Fasto Buru ya jagoranci bakinsa domin yin addu'o'i na musamman domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin addinan kasar nan da duniya bakidaya.

DUBA WANNAN: Kyawawan tagwaye mata sun kafe a kan a kyalesu su auri miji guda, hoto

"Hakan zai kawo cigaba ta fuskar nuna banbancin addini da kabilanci da suka dade suna addabar mutanen mu," Fasto Buru ya fadawa bakin nasa.

A cikin hudubar sa, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya a tsakanin mabanbantan addinai da kabilu dake nahiyar Afrika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel