Kamfen: Babu wanda zai hana Buhari amfani da filin da yake so - Hadimin shugaban kasa

Kamfen: Babu wanda zai hana Buhari amfani da filin da yake so - Hadimin shugaban kasa

A cigaba da shirye-shiryen da ziyarar da shugaba Buhari zai kai jihar Akwa Ibom domin kaddamar da yakin neman zabensa, Sanata Ita Enang, mai taimakawa shugaban kasa a bangaren majalisa, ya ce babu gudu babu ja da baya a amfani da filin wasa na Godswill Akpabio da gwamnatin jihar ta ce ba za a yi taron a wurin ba.

"Zamu cigaba da yin amfani da hanyoyin lallama domin ganin mun yi amfani da filin wasa na Godswill Akpabio domin yin taron mu," a cewar Enang.

A jiya ne Legit.ng ta kawo maku labain cewar gwamnatin Akwa Ibom ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai samu damar yin amfani da filin wasa na kasa da kasa dake Uyo, babban birnin jihar, domin kaddamar da yakin neman zabensa ranar Juma'a ba.

A ranar Juma'a ne shugaba Buhari zai ziyarci jihar Akwa Ibom domin kaddamar da yakin neman zabensa a jihar, kuma jam'iyyar APC ta nemi izinin gwamnatin jihar domin yin amfani da filin wasan.

Kamfen: Babu wanda zai hana Buhari amfani da filin da yake so - Hadimin shugaban kasa

Buhari
Source: UGC

Sai dai gwamnatin jihar ta Akwa Ibom ta sanar da shugaba Buhari cewar sai dai ya yi amfani da karamin filin na garin Uyo ba babban filin wasa na Godswill Akpabio ba kamar yadda ya nema.

Da yake bayyana dalilin hana Buhari amfani da filin wasan, kwamishinan wasanni a jihar Akwa Ibom, Monday Uko, ya ce, "za a fara gasar cin kofin Firemiya na kasa a ranar 13 ga watan Janairu, 2019, a saboda haka ba zamu iya bari taron jama'ar da zasu halarci kamfen din shugaban kasa su lalata mana ciyawar filin wasa ba, musamman a daidai wannan lokaci da kungiyar kwallon kafa ta Akwa United ke buga wasannin gwaji ba.

DUBA WANNAN: Kar a yaudare ku da samun shugabancin kasa - Atiku ya yiwa 'yan yanki kudu maso gabas nasiha

"Kazalika kamfanin Julius Berger dake aikin kula da filin ya bayar da shawarar cewar bai kamata a takura wa ciyawar filin dake shan wahalar yanayi mai tsanani."

Mista Uko ya ce ya zama dole su fito fili suyi bayani domin tuni wasu 'yan siyasa a jihar sun fara bawa lamarin wata fassara ta daban. Sannan ya kara da cewa hatta taron kiristoci da suka shirya zasu yi a filin wasa na Godswill Akpabio bai samu yiwu ba, sai a karamin filin wasa har suka yi taronsu

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel