Abun kai: Cittar da aka noma a Najeriya ta zama zuma a kasuwar duniya

Abun kai: Cittar da aka noma a Najeriya ta zama zuma a kasuwar duniya

- Ministan Noma da Raya Karkara na Najeriya Cif Audu Ogbeh ya ce Najeriya itace na uku a duniya wajen noman citta

- Ministan ya kuma ce cittar Najeriya ta dara da dukkan sauran kasashen duniya inganci a kasuwannin kasa da kasa

- Ya kuma ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta mayar da hankali domin bawa manoma tallafi domin inganta noma a kasar

Ministan Noma da Raya Karkara, Cif Audu Ogbeh ya ce a halin yanzu Najeriya tana cikin kasashen da ke kan gaba wajen noman citta da doya kuma Najeriya ce ta ke ta citta mafi inganci da kyau a kasuwanin duniya.

Ogbeh ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis a Abuja wurin taron masu saka hannun jari na kasa-kasa na Afirka (Africinvest) 2018 inda aka baje kolin wasu kayayakin abinci da ake nomawa.

DUBA WANNAN: 'Yan Siyasar Najeriya basu iya dimokuradiyya ba sam - Farfesa Yakubu

Abun kai: Cittar da aka noma a Najeriya ta zama zuma a kasuwar duniya

Abun kai: Cittar da aka noma a Najeriya ta zama zuma a kasuwar duniya
Source: Depositphotos

A cewarsa, gwamnati tana karfafawa manoma da 'yan kasuwa su rika fitar da citta zuwa kasuwancin duniya kuma ya ce Najeriya itace kasa ta uku a duniya a fannin noman citta bayan China da India amma cittar Najeriya ce mafi ingancin a duniya.

"Gwamnati ta mayar da hankali domin kara yawan cittar da ake nomawa da fitar dashi zuwa kasuwanin duniya tare da tabbatar da cewa an inganta abinda Najeriya ke nomawa ta yadda kasashen duniya za su amince dashi.

Alhaji Azeez Olumuyiwa, Direktan sarrafa kayan abinci da kasuwanci ne ma'aikatar noma ne ya wakilci Ogbeh a wajen taron.

Ministan ya ce shuagaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shirin da a cikin kankanin lokaci za a inganta ayyukan noma a Najeriya a karkashin Agricultural Promotion Policy (APP) 2016 zuwa 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel