'Karancin albashi na N30,000 ba zai yiwu ba sam a jihohi ko nan da shekaru 10'

'Karancin albashi na N30,000 ba zai yiwu ba sam a jihohi ko nan da shekaru 10'

- Babu yuwuwar biyan karancin albashi dubu talatin nan da shekara goma

- Ko jihohi zasu dinga aro kudi don biyan ma'aikata ne?

- Yakamata ma'aikata suyi hakuri da gwamnati

Karancin albashi na: 'N30,000 din nan na albashi ba zai yiwu ba sam-sam'

Karancin albashi na: 'N30,000 din nan na albashi ba zai yiwu ba sam-sam'
Source: UGC

Tsohon babban akanta daga jihar Bauchi, Garba Ali-Maigumau, a ranar laraba yace gwamnatocin jihohi bazasu iya biyan ma'aikata dubu talatin ba a matsayin karancin albashi nan da shekara goma masu zuwa.

Ali-Maigumau, wanda ya sanar da hakan a tattaunawar shi da manema labarai, yace: "Ina sanar daku hakane a matsayin dan cikin gida; Mutane nata maganar dubu talatin, amma ba zai yuwu ba, ba zai yi aiki ba. Misali a jihar Bauchi, akwai ma'aikata 105,000.

Idan aka biya su karancin albashi dubu talatin, ace ma kowa na matsayi daya ne, mutane 105,000 zaka biya Naira biliyan 3.150 kenan.

Toh wannan shine dolen ma, banda alawus. Alawus din ma yafi albashin. Mutum na matsayi na hudu da albashi dubu talatin, ga kuma alawus dinshi dubu hamsin. Zai dinga karbar dubu tamanin kenan. Toh dubu tamanin sau 105,000.

Nasan zai bada sama da Naira biliyan 10. A ina za'a samo biliyan 10 din? A nan jihar Bauchi, mafi yawan kudin da muke samu daga tarayya shine biliyan 4, a hada da Naira biliyan 3 na kananan hukumomi. Kaga miliyan 7 kenan. "

"Toh Idan zamu biya ma'aikatan jihar da kananan hukumomi da biliyan 10, a ina zamu samo Naira biliyan 3? Yana nufin zamu zauna muyi ta aron kudi daga bankuna don biyan albashin ma'aikatan jihar mu duk wata ne? "

DUBA WANNAN: Ta tsaga hannunta da reza da sunan soyayya, leka kuji shi kuma gogan ko me yayi wa masoyiyar

Kamar yanda yace, babu jihar da a duk fadin kasar nan tayi alkawarin biyan dubu talatin a matsayin karancin albashi.

Mista Ali-Maigumau, ya shawarci ma'aikata dasu yi hakuri da gwamnati saboda bazata iya biyan karancin albashin ba a halin da ake ciki.

Yace za'a iya dai kyautatawa ma'aikatan dai ko a nan gaba.

"Jami'ai da yan kungiyar kwadagon sun San abinda ke faruwa. Sun sani, kawai suna nuna basu sani bane saboda yawancin shuwagabannin kungiyar kwadagon ma'aikatan gwamnati ne. Don haka bazasu ce basu san abinda ke faruwa na rashin kudin Gwamnatin ba," inji shi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel