Yawan barbada foda yana jawo cututtuka inji Masana kiwon lafiya

Yawan barbada foda yana jawo cututtuka inji Masana kiwon lafiya

Binciken da Masana su kayi ya nuna cewa Mutane da ke yawan barbada foda da sauran kayan kwalliya su na iya fama da cututtuka irin su hawan jini da cutar daskarewar jini da sauran cututtuka na fatar jiki.

Yawan barbada foda yana jawo cututtuka inji Masana kiwon lafiya

Yawan kwalliya na jawowa 'Yan mata cututtuka inji Masana
Source: UGC

Kwanakin baya ne mu ka samu labari cewa ‘Yan mata na fama da barazanar cututtuka irin su kansa na daskarewar jini da hawan jini a sakamakon sinadaran da ke cikin kayan kwalliya irin su foda, jan baki da ja gira da su kwalli.

Dakta Alex Adeniyi, wanda wani Masani ne a harkar cututtukar fata, ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa akwai sinadaran da ke cikin kayan kwalliyan mata da ke dauke da abubuwan da ke sa cuta idan ana yawan amfani da su.

KU KARANTA: Osinbajo ya bayyana abin da ya sa furfura ya fito masa

Wannan babban Dakta yace yawan barbada foda a kumatu da su gazal a idanu ka iya jawowa mutum borin jini da wasu cututtuka na fata. Haka zalika kuma irin wadannan kayan kwalliya su kan jawo kuraje a jikin ‘Yan mata.

Wata Baiwar Allah wanda ta karanci harkar kwalliya, Pamale Obunwa, ta bayyana cewa dole mata su rika la’akari da irin kayan kwalliyar da su ke amfani da su. Akwai kayan adon da ke jawo Budurwa ta tsufa da wuri inji Masanan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel