Yabon goni: IBB ya jingine banbancin siyasa, ya yabawa Buhari

Yabon goni: IBB ya jingine banbancin siyasa, ya yabawa Buhari

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya ajiye banbancin siyasa a gefe ya yi ruwan kalaman yabo ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a yayin da ya cika shekaru 76 da haihuwa.

Babangida, a sakon da ya sakawa hannu da kansa, ya bayyana shugaba Buhari a matsayin abun koyi ga 'yan Najeriya.

A ranar Litinin, 17 ga watan Disamba, ne shugaba Buhari zai cika shekaru 76 da haihuwa.

A 'yan kwankin baya bayan nan, Babangida ya kasance daya daga cikin masu sukar gwamnatin tarayya da jam'iyyar APC tare da yin kira ga shugaba Buhari da ya ajiye batun sake neman takara domin bawa matasa damar shugabantar Najeriya. Kazalika ya bukaci 'yan Najeriya da kar su kada kuri'unsu ga shugaba Buhari.

A takardar taya murnar ta IBB, ya bayyana cewar shugaba Buhari abun koyi ne ga matasa da ma manya dake da burin gwagwarmaya irin ta siyasa, musamman kokarinsa na cigaba da tafiyar da Najeriya a matsayin kasa daya mai al'umma daya.

Yabon gwani: IBB ya jingine banbancin siyasa, ya yabawa Buhari

IBB da Buhari
Source: Facebook

"Ka samu gagarumar nasara a bangaren yaki da cin hanci da ta'addanci da kuma inganta harkokin tsaro da tattalin arziki.

"Abun a yaba maka ne yadda a shekaru 76 Ka iya jure dukkan kalubalen shugabanci tare da iya tafiyar da gwamnati cikin gaskiya da rikon amana, ba tare da nuna bangarenci ba.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya fadi abinda Buhari ya yi da babu shugaba a duniya da ya taba yi

"Ina mai taya ka murnar dukkan nasarorin da ka samu a gwamnatinka da ma rayuwar ka, musamman gaskiya da rikon amana da ka nuna a dukkan matakan da ka samu kan ka," kamar yadda IBB ya fada a cikin sakon nasa.

Kazalika, tsohon shugaban ya taya uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, da 'ya'yansa murnar zagayowar ranar haihuwar shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel