Na jira awa goma kan gawar dan sandan da na kashe da hannuna - Basaraken Tibi

Na jira awa goma kan gawar dan sandan da na kashe da hannuna - Basaraken Tibi

- Shugaban al'ummar Tibi na garin Odeda da ke jihar Ogun, Jonathan Tsekar ya kashe wani jami'in dan sanda

- Ya kashe dan sandan mai suna Gbenga Adeboyejo ne sakamakon fada da su kayi bayan dan sandan ya bashi aiki amma bai kammala a akan lokaci ba

- Bayan ya kashe dan sanda, ya zauna tare da gawar dan sandan a gonarsa na tsawon sa'o'i 10 kafin ya birne shi

Jonathan Tsekar, Sarkin al'ummar Tibi a garin Opeji da ke karamar hukumar Odeda na jihar Ogun ya bayyana yada ya kashe wani jami'in dan sanda da ke aiki a garinsu.

Punch ta ruwaito cewa Tsekar ya kashe dan sandan mai suna Gbenga Adeboyejo ne saboda rashin jituwa da ta faru tsakaninsu sakamakon cikini gawayyi. Basaraken ya kashe Adeboyejo na wata gona da ke garin a ranar 27 ga watan Nuwamba kuma ya birne shi tare da wayar salulansa.

Majiyar Legit.ng ta tattaro cewa dan sandan yana zauna a garin ne shi kadai yayin da iyalansa ke zama a Ilorin. An ruwaito cewar lamarin ya afku ne kwanaki biyu bayan Adeboyejo ya dawo daga ganin iyalansa a Ilorin.

City Round ta ruwaito cewa mahaifin dan sandan, Joseph ya shigar da kara a caji ofis bayan ya gaza samun dansa a waya. Hakan yasa aka shigar da karar bacewar dan sandan kuma aka fara bincike.

Na jira awa goma kan gawar dansandan da na kashe da hannuna
Na jira awa goma kan gawar dansandan da na kashe da hannuna
Asali: Twitter

An kama Tsekar ne saboda bayannan da aka samu wajen mahaifin dan sandan, Joseph da kuma wasu mazauna unguwar.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

A hirar da ya yi da manema labarai, Tsekar mai shekaru 32 a duniya kuma dan asalin jihar Benue ya ce Adeboyejo ya bashi kwangilar samar masa gawayi a ranar 26 ga watan Oktoba kuma ya biya shi N97,000 cikin N150,000 da suka amince.

Tsekar ya ce, "A ranar 26 ga watan Oktoba, Adeboyejo ya bani N97,000 domin in sare itace in sarrafa masa gawayi. Na fara aikin sai ya ce min zai tafi gida ya dawo. A lokacin da ya dawo bayan makonni 2, na fara aikin amma ban kammala ba.

"Bayan dawowarsa mun tafi gona inda na nuna masa aikin amma bai gamsu ba saboda ban gama ba. Hakan yasa ya fara min tsawa har ya dauki sanda ya fara duka na, nayi kokari na karbi sandan inda nima na buga masa.

"Nayi niyyar dukkansa da sandan a jiki amma ya kauce na bugi kansa kuma ya fadi nan take kuma na lura ya dena motsi. Na zauna tare da shi har zuwa karfe 7 na yamma ina tunanin zai farfado amma bai tashi ba.

"Na haka rami na binne shi tare da wayarsa saboda bana son a gano cewa ni ne na kashe shi. Ina zaune a kauyen tun 2003 amma ban taba aikata wani laifi ba. Ni ne shugaban al'ummar Tibi a garin Odeda."

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu idan an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel