Gwamnati Buhari ta daure manyan 'yan siyasa 6 tun bayan hawanta mulki

Gwamnati Buhari ta daure manyan 'yan siyasa 6 tun bayan hawanta mulki

A shekarar 2015 ne shugaba Buhari ya samu nasarar kayar da gwamnatin PDP karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Gabanin zaben shekarar 2015, Buhari ya yi yakin neman zabe ne da muhimman abubuwa 3; tsaro, yaki da cin hanci da rashawa, da gina tattalin arzikin Najeriya.

Duk da wasu na korafi kan cewar gwamnatin shugaba Buhari na nuna son kai a binciken da take yi na barna da karya tattalin arzikin kasa a gwamnatocin, gwamnatin ta shi tayi nasarar yin abinda a baya ake tunanin ba zai taba yiwuwa ba.

A yayin da shekarar 2018 ke kokarin yin bankwana, mun yi waiwaye a kan irin manyan 'yan siyasa da gwamnatin Buhari tayi nasarar tisa keyar su zuwa gidan yari bayan samun su da laifin cin hanci.

1. Joshua Dariye: Sanata kuma tsohon gwamna, an gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhumar sa da karkatar da kimanin N1.162 daga asusun jihar Filato lokacin da yake gwamna. Tun shekarar 2007 aka gurfanar da shi amma shari'ar ta ki cigaba saboda kokarin Dariye m ganin ba a hukunta shi ba.

A ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 2018 ne mai shari'a, Jastis Adebukola Banjoko, ta yankewa tsohon gwamna Dariye hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari.

Manyan 'yan siyasa 6 da gwamnatin Buhari ta daure

Joshua Dariye
Source: Depositphotos

2. Jolly Nyame: Kamar tsohon gwamna Dariye, kotu ta yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu tun shekarar 2007 bisa tuhumar sa da karkatar da N1.64bn lokacin da yake gwamna.

Manyan 'yan siyasa 6 da gwamnatin Buhari ta daure

Jolly Nyame
Source: Depositphotos

3. Jonah Jang: Tsohon sojan sama, tsohon gwamna, kuma Sanata mai ci, Jonah Jang, ya shafe tsawon kwanaki 8 a gidan yari kafin daga bisani a bayar da shi beli.

Jang na fuskantar tuhuma 12 a gaban kotu a kan wawurar N6.3bn daga asusun jihar Filato lokacin da yake gwamna.

Manyan 'yan siyasa 6 da gwamnatin Buhari ta daure

Jonah Jang
Source: UGC

4. Ramalan Yero: Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Yero ya shafe kusan sati a wani gidan yari dake Kaduna.

Yero, ba tare da ya taba yin takara ba, ya zama kwamishina, mataimakin gwamnan kafin daga bisani ya zama gwamna bayan mutuwar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ibrahim Yakowa, a watan Disamba na shekarar 2012.

Manyan 'yan siyasa 6 da gwamnatin Buhari ta daure

Ramalan Yero
Source: Depositphotos

An tsare tsohon gwamna Yero tare da tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, Abubakar Gaya-Haruna, da kuma tsohon kwamishinan lantarki, Nuhu Sumo Wya, bayan hukumar EFCC ta gurfanar dasu gaban kotu da laifin almundahana da zamba.

5. Ayodele Fayose: Tsohon gwamna a jihar Ekiti, Fayose ya yi hutun karshen mako a wani gidan yari dake Ikoyi a jihar Legas bayan ya gaza cika sharudan belin da kotu ta gindaya masa.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Fayose bisa tuhuma 11 masu nasaba da hada baki domin yin zambar kudi da yawansu ya kai N2.2bn.

Manyan 'yan siyasa 6 da gwamnatin Buhari ta daure

Fayose
Source: UGC

Fayose ya samu beli a ranar Laraba, 24 ga watan Oktoba.

6. Sule Lamido: Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Lamido ya yi hutun karshen mako a gidan yari na Kurmawa dake garin Kano bayan an daga sauraron karar sa kuma lauyan EFCC ya shaidawa kotu cewar basu da wurin da zasu ajiye tsohon gwamnan ofishinsu.

Manyan 'yan siyasa 6 da gwamnatin Buhari ta daure

Sule Lamido
Source: Twitter

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Lamido tare da dan cikinsa bisa tuhumar su da badakalar fiye da biliyan daya da suka karba daga hannun 'yan kwangila ta haramtacciyar hanya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel