Gwamnatin Buhari na son kara shekarun ritayar malaman makaranta
- Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce gwamnatin shugaba Buhari tana goyon bayan kara shekarun ritayan malamai
- Minstan ya ce karin shekarun zai bawa malaman damar inganta ayyukansu da darajar ilimi a makarantu
- Ministan ya yi kira ga majalisa ta amince da bukatan karin shekarun murabus din kamar yadda wasu kasashen duniya suka kara nasu
A yau, Alhamis 12 ga watan Disamba ne ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana goyon kara shekarun ritayan malaman makarantu daga shekaru 60 zuwa 65.
Ministan ya yi wannan bayanin ne a wani taron jin ra'ayin al'umma da aka shirya domin neman ware malaman makarantu daga shekarun ritaya na sauran ma'aikatan gwamnati da kwamitin majalisa na Ilimi da ayyuka gwamnati ta shirya.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Kwanan nan ta'addanci a Zamfara zai zama tarihi - Buratai ya ci al washi
Ministan ya ce wannan yunkurin zai inganta darajar ilimin frimare da sakandare a kasar.
Mr Adamu ya sanar da kwamitin cewa Kungiyar Malamai na Kasa (NUT) ta shigar da bukatar canja sabon shekarun ritayan na malamai ga ma'aikatar Ilimi da kuma majalisar tarayya domin neman amincewarsu.
Ya ce ana neman karin shekarun ne domin bawa malaman damar su inganta ayyukansu da kuma yunkurin samar da malamai masu kwarewa da nagarta a makarantun Najeriya.
"Kamar yadda kasashen India, Canada da Belgium suka kara shekarun ritaya na malaman makaranta, suma malaman Najeriya na bukatar ayi musu wannan karin.
"Muna kira ga majalisa ta amince da kudirin dokar saboda ma'aikatar ilimi tana goyon bayan kudirin karin shekarun ritaya na malaman makarantan," inji Adamu
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng