Mabiya Shi'a sun gudanar da zanga-zangar cikar shekara 3 da tsare Zakzaky

Mabiya Shi'a sun gudanar da zanga-zangar cikar shekara 3 da tsare Zakzaky

Mabiya Shi'a a Najeriya sunyi zanga-zangar zaman lafiya domin korafi kan tsare shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky na tsawon shekaru uku da tunawa da kisar kiyashi da aka yiwa 'yan kungiyar a Zaria.

Masu zanga-zangar sunyi tattaki zuwa sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja a yau Laraba dauke da alluna masu sakonnin bukatar gwamnati ta saki shugabansu da aka tsare tun Disambar 2015.

A yayin da ya ke jawabi ga masu zanga-zangar, sakataren IMN, Abdullahi Musa ya ce an tsare El-Zakzaky ne ba tare da wani kwakwaran dalili ba.

Mabiya Shi'a sun gudanar da zanga-zangar cikar shekara 3 da tsare Zakzaky
Mabiya Shi'a sun gudanar da zanga-zangar cikar shekara 3 da tsare Zakzaky
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Laifi ne saduwa a cikin mota - Hukumar 'yan sanda ta karyata jami'inta

Ya ce: "A ranar 12 ga watan Disambar 2015, Rundunar Sojin Najeriya ta kaiwa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky hari da sunan kafa an tare hanya. An kwashe sa'o'i 48 ana harin inda aka kashe mutane fiye da 1000 ciki har da mata da yara.

"Wadanda aka kashe sun hada yaran Sheikh Zakzaky wato Ali, Hamid da Humaid, kuma bayan harin gwamnatin Buhari ta tsare El-Zakzaky ba tare da kulawa mai kyau ba."

A cewar Musa, sojojin sun kone mutane da rayyukansu ciki har da 'yar uwar Zakzaky. Ya kuma zargi Sojin da birne gawarwakin a wani boyeyen waje a Mando da ke Kaduna.

Ya cigaba da cewa: "Shekaru uku bayan kisar kiyashin da aka yi a Zaria da kuma rahoton da kwamitin bincike ta fitar a Yulin 2016, gwamnati ta ki hukunta wadanda suka aikata wannan kisan kiyashin.

Sai dai ya ce kungiyar ba za tayi kasa gwiwa ba har sai gwamnatin ta saki Shiekh Ibraheem Zakzaky da matarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel