Za ayi jana’izar dakarun Sojojin Najeriya 100 da mayakan Boko Haram suka halaka

Za ayi jana’izar dakarun Sojojin Najeriya 100 da mayakan Boko Haram suka halaka

Rundunar Sojan kasa ta Najeriya ta kammala shirin gudanar da jana’izar dakarunta guda dari da suka ransu a hannun mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a yayin wani harin kwanta bauna da yan Boko Haram suka kai musu.

A watan data gabata ne mayakan Boko Haram suka kai ma dakarun bataliya ta 157 na rundunar Sojan kasa a kauyen Matele na jahar Borno, inda suka kashe Sojoji da dama daga cikinsu har da kanana da hafsoshin Soja.

KU KARANTA; Buratai ya yiwa dakarun Sojoji kashedi da tsoma baki cikin siyasar 2019

Jaridar Punch ta ruwaito wata daga cikin matan Sojojin da aka kashe data nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da wannan shiri na binne Sojojin, inda tace a ranar Juma’a za’a gudanar da jana’izar a garin Maiduguri.

Majiyar Legit.com ta ruwaito matar tana cewa “An gayyaceni zuwa taron binne Mijina tare da sauran abolansa da aka kashe a filin daga, a ranar Juma’a za’a binnesu a Maiduguri, amma bamu san adadin gawarwakin da za’a binne ba, kuma rundunar soja bata fada mana ba.”

Sai dai wajin hafsan Soja mai mukamin Kanal ya bayyana ma majiyarmu cewa da gangan aka shirya gudanar da jana’izar a boye, domin gudun fallasa adadin Sojojin da suka rayukansu a wancan hari na Boko Haram.

“Kun san Janar Buratai yace Sojoji 23 aka kashe, sa’annan yace Sojoji 31 ne suka jikkata a sanadiyyan harin, amma mu mun san ba gaskiya bane, akalla an kashe Sojoji 100, don haka aka shirya binnesu a tare da gayyatar kowa ba sai iyalansu don kada a fallasa adadinsu.”

Sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin kaakakin rundunar Sojojin kasa, Birgediya Sani Kuka Sheka yaci tura, sakamakon bai amsa wayar da aka kirasa ba, kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel