2019: Za mu sakawa wadanda suka yiwa jam'iyya hidima - Buhari ga magoya bayansa

2019: Za mu sakawa wadanda suka yiwa jam'iyya hidima - Buhari ga magoya bayansa

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa magoya bayansa alkawarin cewa ba za a manta da su ba bayan lashe zaben 2019

- Shugaban kasar ya ce za a saka wa dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa wajen cin nasarar tare da yiwa jam'iyya biyaya

- Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a fadar sa ta Aso Villa a wajen kadamar da wata shiri da kungiyar magoya bayansa suka bullo da shi

2019: Za mu sakawa wadanda suka yiwa jam'iyya hidima - Buhari ga magoya bayansa
2019: Za mu sakawa wadanda suka yiwa jam'iyya hidima - Buhari ga magoya bayansa
Asali: Depositphotos

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatarwa magoya bayansa cewa a shekarar 2019, za a sakawa dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa tare da biyaya ga jam'iyya idan aka cimma nasara.

A jawabin da ya yi wajen kadamar da 'Together Nigeria' da Buhari Support Organisation (BSO) suka kafa domin yakin neman zabensa na 2019 a fadar Aso Rock Villa, shugaban kasar ya tabbatar musu da cewa ba za a manta da su ba.

DUBA WANNAN: Borin kunya ce ta sanya Atiku rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya - APC

"Ga dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa wajen ganin munyi nasara, na san wasu daga cikin ku sunyi fushi ... Amma ina son in tabbatar muku wannan karon wadanda su kayi aiki da biyaya ga jam'iyya za su samu sakamako mai kyau," inji shi.

Wannan jawabin na shugaba Muhammadu Buhari ya sanya dandazon magoya bayansa da suka hallarci taron murna da tafi.

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari tare da manyan 'yan Najeriya da dama sun samu hallartan taron. Mutane da dama sun yi ta bayyana goyon bayansu ga shugaban kasar a wajen taron.

Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal da aka tsige a Oktoban 2017 saboda samunsa da almundahana cikin kwangilar cire ciyawa bayan majalisa tayi bincike yana daya daga cikin wadanda suka hallarci taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel