Sukar Obasanjo: Fasto Omokri ya kafa wa Garba Shehu hujja da Qur'ani

Sukar Obasanjo: Fasto Omokri ya kafa wa Garba Shehu hujja da Qur'ani

An samu barkewar cece-kuce tsakanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, da fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan batun zaben shekarar 2019.

A yau Laraba ne Garba Shehu, yayin magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, ya bayyana cewar Obasanjo ya rude saboda goyon bayan takarar Atiku Abubakar a karkashin jam'iyyar PDP bayan a baya ya yi ikirarin cewar Allah ba zai yafe masa ba idan ya goyawa Atiku baya.

A cewar Shehu, "tsohon shugaban kasa Obasanjo zai iya kushe yau amma gobe ya ce babu wanda ya fika.

"Ya kan saka Allah cikin zancensa idan ya fuskanci ya tafka kuskure. Tuni mun saba da halinsa, a saboda haka ko damuwa da kalamansa bama yi.

"Bamu manta cewar Obasanjo da kansa ya kira manema labarai ya yaga katin shaidar sa na zama mamba a jam'iyyar PDP. Babu wani da zai yi ya bamu mamaki," a cewar Garba Shehu.

Sukar Obasanjo: Fasto Omokri ya kafa wa Garba Shehu hujja da ayar Qur'ani
Fasto Omokri
Asali: Instagram

Sai dai, Omokri (Fasto a kasar Amurka) ya yiwa Garba Shehu raddi a shafinsa na Tuwita tare da yi masa tunin yadda a shekarar 2003 Obasanjo ya nada shi mataimaki na musamman a bangaren yada labarai.

DUBA WANNAN: Muhawara: Osinbajo zai iya wakiltar Buhari - Babban lauya, Itse Sagay

Omokri ya kara da cewar ya karanta littafin Alqur'ani mai girma, kuma ya san cewar abinda Garba Shehu ya aikata na cin mutuncin Obasanjo, mutumin da ya taba bashi aiki, ya saba da koyarwa irinta Alqur'ani.

"Irin kalaman dake fitowa daga fadar shugaban kasa abin kunya ne, musamman ganin sa hannu Garba, mutumin da Obasanjo ya bawa aiki, a kan kalaman.

"Ya kai Garba Shehu, baka da da'a. Na karanta Alqur'ani, abinda kayi ya saba da koyarwar sa," a cewar Omokri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng