Borin kunya ce ta sanya Atiku rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya - APC

Borin kunya ce ta sanya Atiku rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya - APC

- Jam'iyyar APC ta ce dan takarar shugabacin kasa, Atiku Abubakar ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ne domin ganin idon mutane

- APC ta gargadi 'yan Najeriya da jami'an tsaro cewa jinkirin da Atiku ya yi alama ce da ke nuna yana shirya wata makirci gabanin babban zaben na 2019

- APC tayi kira da hukumomin tsaro su kasance cikin shiri domin dakile duk wata barazana ko sharri da jam'iyyar ta PDP za ta iya bullo da shi

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta bukaci 'yan Najeriya suyi takatsantsan da jam'iyyar PDP da dan takakarar shugabancin kasar ta, Atiku Abubakar musamman a yanzu da babban zaben 2019 ke matsowa.

A sanarwa da ta fito daga bakin sakataren yada labarai na kasa na APC, Lanre Issa-Onilu, jam'iyyar tayi ikirarin cewa Atiku bai yi niyyar rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ba.

Atikun dai ya sanya hannu a kan yarjejeniyar ne a ranar Laraba, kwana guda bayan sauran 'yan takarar shugabancin kasar ciki har da shugaba Muhammadu Buhari sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar.

Borin kunya ce ta sanya Atiku rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya - APC
Borin kunya ce ta sanya Atiku rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya - APC
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: 2019: An ware 'yan takarar shugaban kasa biyu daga shiga muhawarar da za a fafata

Atiku ya ce kwamitin da ta shirya taron ba ta gayyace shi bane shi yasa bai hallarci taron ba sai dai shugaban taron kuma tsohon shugaban kasa, Abdulsalami ya karyata wannan zance daga bisani dai an ce an samu matsalar sadarwa ne tsakanin masu shirya taron da ofishin PDP na kasa

Sai dai a sanarwar da APC ta fitar, ta ce Atiku ba shi da wani uzuri na kwakwara tunda a lokaci guda aka mika gayyatar ga dukkan 'yan takarar shugabancin kasar dukkan jam'iyyun.

Sanarwar ta ce, "Ya fito fili karara cewa dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar bai yi niyyar saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba gabanin babban zaben 2019.

"Rattaba hannu a kan yarjejeniyar da ya yi daga bisani shima saboda borin kunya ce da kuma tir da al'umma su kayi bisa rashin sanya hannun nasa. Ya kamata mu lura cewa wannan alama ce da ke nuna PDP na Atiku na shirya wata makirci gabanin zaben."

Jam'iyyar ta APC ta yi kira da hukumomin tsaro su kasance cikin shiri a ko da yaushe domin dakile duk wata sharri da fitina da jam'iyyar na PDP ke shiryawa domin babban zaben na 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164