Muhawara: Osinbajo zai iya wakiltar Buhari - Babban lauya, Itse Sagay
Shugaban kwamitin bawa shugaban kasa shawara a kan yaki da cin hanci (PACAC), Farfesa Itse Sagay, ya bayyana cewar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, zai iya wakiltar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a wurin muhawarar 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2019.
Da yake magana da manema labarai, Sagay ya ce muhawarar ba ta nuna zakin baki ba ce, muhawara ce a kan manufar jam'iyyu ga Najeriya.
"Me zai hana? mataimakin shugaban kasa zai iya wakiltar shugaban kasa idan haka gwamnati ke so. Muhawara ba 'yar kure ba ce, magana ce ta irin manufar da jam'iyyar dan takara ke da ita ga kasa.
"Idan har jam'iyya zata iya nada kakakin jam'iyya ya wakilce ta, me zai hana gwamnati ta wakilta mataimakin shugaban kasa ya wakilce ta tunda fadar shugaban kasa dai daya ce," a kalaman Farfesa Sagay.

Asali: UGC
Kungiyar tsara muhawara a tsakanin 'yan takara ta kasa (NEDG) da kuma cibiyar watsa labarai ta Najeriya (BON) sun lissafa jam'iyyun Najeriya 5 da za a fafata muhawara da 'yan takarar su na shugaban kasa a zaben 2019.
A jawabin da sakataren NEDG, Eddi Emesiri, ya fitar ya ce jam'iyyun da za fafata mahawarar da su sune; ACPN, ANN, APC, PDP da YPP.
DUBA WANNAN: APC ba zata taba zama lafiya ba - Ministan Sadarwa
Hakan ya nuna muraran cewar 'yan takarar da su buga a muhawarar sune; Atiku Abubakar, Muhammadu Buhari, Oby Ezekwesili, Fela Durotoye, da Kingsley Moghalu.
Za a gudanar da mahawarar 'yan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Juma'a, 14 ga watan Disamba, 2018, yayin da za ai na shugaban kasa ranar Asabar, 19 ga watan Janairu, 2019.
Ana sa ran hukumar BON tare da takwarorinta zasu nuna mahawarar kai tsaye a kafafe da cibiyoyin watsa labarai.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng