Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar jihar Yobe ya yi murabus, an zabi sabo
Kakakin majalisar jihar Yobe, Adamu Dala-Dogo ya yi murabus daga mukaminsa.
Premium Times ta ruwaito cewa Mr Dala ya aike da wasikar murabus dinsa ga majalisar inda mataimakin majalisa, Ibrahim Kurmi ya karanto a zauren majalisar.
Ya yiwa takwarorinsa godiya bisa damar da suka bashi na rike mukamin kakakin majalisar.
Majalisar ta maye gurbin Mr Dala-Dogo da Zannah Machina bayan Ibrahim Kallalawa ya gabatar da kudirin zaben sabon kakakin majalisa kuma Ishaku Daya ya goyi bayan kudirin.
DUBA WANNAN: 2019: An ware 'yan takarar shugaban kasa biyu daga shiga muhawarar da za a fafata

Asali: Twitter
Mr Dala-Dogo da ke wakiltan mazabar Karasuwa a majalisar ya kwashe shekaru bakwai yana aiki a matsayin kakakin majalisar.
Jagoran majalisar, Usman Kabaruma mai wakiltar karamar hukumar Tarmuwa ya shaidawa manema labarai cewa Mr Dala-Dogo ya yi murabus ne domin ra'ayin kansa kamar yadda NAN ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng