Tsohon gwamna da 'yan takarar gwamna 3 sun koma APC a Jigawa
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Ali Sa'ad Birnin Kudu ya fice daga PDP ya koma APC
- Wasu 'yan takarar gwamna biyu daga PDP tare da wata 'yar takarar guda daga jam'iyyar SDP suma sun koma APC
- Gwamna Mohammed Badaru na jihar ne ya karbe su a madadin shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Barristewr Ali Sa'ad Birnin Kudu da wasu 'yan takarar gwamna guda uku sun fice daga jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da Social Democratic Party (SDP) sun koma jam'iyyar APC.
Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan takarar gwamna biyu da suka fice daga jam'iyyar PDP sune Kabiru Tijjani Kiyawa da Mohammed Danladi Auyo sai kuma Ramatu Sabo Elleman daga jam'iyyar SDP.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: 2019: Daya daga cikin manyan hadiman Kwankwasiyya ya koma Gandujiyya
Tsaffin kwamishinoni da su kayi aiki karkashin gwamnatin jam'iyyar PDP da ta gabata a jihar suma suna daga cikin dimbin mutanen da suka sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki a jihar wato APC.
Gwamnan jihar, Mohammed Badaru Abubakar shine wanda ya karbi wadanda suka sauya shekar a Dutse a madadin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Comrade Adams Oshiomhole.
Kazalika, a yau ne Gwamna Mohammed Badaru Abubakar ya kaddamar da yakin neman zabensa na takarar gwamna a 2019 karkashin jam'iyyar APC a babban birnin jihar Jigawa, Dutse.
Taron kaddamar da yakin neman zaben ya samu hallarci jiga-jigan jam'iyyar APC na jihar, mukarraban gwamnan, shugabanin jam'iyya, mambobin jam'iyyar da dimbin magoya bayan gwamna Badaru Abubakar.
Gwamnan ya yi alkawarin cigaba da ayyukan alkhairi da ya fara aiwatar wa a jihar inda aka sake zabensa karo na biyu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng