An sace matan tsohon mataimakin shugaban karamar hukuma da diyarsa a Zamfara

An sace matan tsohon mataimakin shugaban karamar hukuma da diyarsa a Zamfara

- 'Yan bindiga a Zamfara sun sace matan tsohon mataimakin ciyaman din karamar hukumar Shinkafi biyu da 'yar sa guda daya

- 'Yan bindigan sun kuma kashe jami'an tsaron sai kai na Civilian JTF guda uku sakamakon musayar wuta da su kayi da 'yan bindigan

A jiya Litinin ne wasu 'yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara inda suka kashe jami'an tsaro na sai kai 'Civilian JTF' 3 kuma su kayi garkuwa da matan tsohon mataimakin ciyaman din karamar hukumar Shinkafi, Bello Birnin Yero da diyarsa guda.

'Yan bindiga sun sace 'yan sa kai 3 a Zamfara, sun sace mata
'Yan bindiga sun sace 'yan sa kai 3 a Zamfara, sun sace mata
Asali: Twitter

Daily Nigerian ta ruwaito cewa wani shaidan ganin ido, Isah Adamu ya ce 'yan bindigan da adadin su ya kai 100 sun iso garin misalin karfe 12 na dare kuma suka nufi gidan dan siyasar su kayi awon gaba da matansa biyu da diyarsa daya.

DUBA WANNAN: Yadda na lashe zaben shugabancin kasa na 2015 - Buhari

"A yayin da aka sanar da jami'an JTF, sun bi sahun 'yan bindigan cikin gaggawa domin ceto matan amma 'yan bindigan suka kashe uku cikinsu yayin da suke musayar wuta kuma suka tsere da matan uku."

"Muna fuskantar barazana daga wajen 'yan bindigan a kullum, muna bukatar karin jami'an tsaro da za su kakkabo su daga dajin da suke buya. Suna kusa da mu ne a kan iyakan jamhuriyar Nijar," inji shi.

Anyi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu amma hakan ba ta yiwu ba a lokacin da ake rubuta wannan rahoton.

A watan da ya gabata, Gwamna Abdulaziz Yari ya amince da daukan sabbin jami'an Civilian JTF 8,500 a masarautu 17 da ke jihar domin su taimakawa jami'an tsaro wajen yaki da 'yan ta'addan da suka addabi jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164