Takaitaccen tarihin sabon Shugaban Majalisar dokokin da aka zaba a Katsina
A makon da ya gabata ne Honarabul Tasi’u Musa Maigari ya zama sabon Kakakin Majalisar dokoki na Jihar Katsina. An zabi Musa Maigari ne bayan tsohon Kakakin Majalisar Jihar ya zama ‘Dan Majalisar Tarayya.

Asali: UGC
Mun kawo maku kadan daga cikin tarihin wannan Shugaban Majalisa da aka samu a Jihar Katsina kamar yadda mu ka tsakuro daga Jaridar Daily Trust. Ga kadan daga labarin rayuwar sa nan:
- Haihuwa
An haifi Musa Maigari a cikin Watan Afrilun 1966 a wani Kauye da ake kira Fuyumi a cikin Garin Zango a Yankin Daura. A nan Yankin Tasiu Maigari yayi karatun Firamare har zuwa 1978 inda ya wuce Garin Kaduna domin cigaba da ilmi.
KU KARANTA: Wani 'Dan majalisar tarayya na Katsina ya fice daga APC ya koma PDP
2.Karatun Boko
Rt. Hon. Maigari yayi Sakandare a Makarantar da ake kira Sardauna Memorial College (SMC) a Kaduna daga 1987 zuwa 1983, bayan nan kuma ya samu shaidar Difloma a Kaduna Polytechnic inda yayi karatu daga 1985 har zuwa shekarar 1988.
3.Aiki
Tasiu Maigari ya fara aiki ne a wani Kamfani a Fuyuni tun 1988 inda ya zama Darekta. Daga baya ya shiga siyasa har aka zabe sa ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Zango a Jihar Katsina. Maigari shi ne Shugaban kwamitin lafiya a Majalisar.
4.Majalisa
Kwanaki ne Honarabul Ibrahim Dikko wanda yake wakiltar Matazu ne ya nemi a nada Tasi’u Musa Maigari ya maye gurbin Abubakar Yahaya Kusada inda Honarabul Sani Lawal da sauran ‘Yan Majalisa su ka amince da hakan ba tare da hamayya ba.
Idan ba ku manta ba, Abubakar Yahaya Kusada ya zama ‘Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ingawa/Kusada/Kankia a zaben da aka yi kwanan nan. Kafin Kusanda, Aliyu Sabiu Maduru ya rike Majalisar kafin a tsige sa a farkon shekarar 2017.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng