Wata Mata Musulma ta bayar da tallafi ga Mata Zaurawa domin Bikin Kirsimeti
- Wata Mata Musulma ta yiwa Kiristoci Zaurawa goma ta arziki domin shagulgulan Bikin Kirsimeti
- Hajiya Ramatu Tijjani ta nemi hadin kai a tsakanin mabiya addinan kasar nan domin tabbatar da zaman lafiya
- Hajiya Ramatu ta nemi gwamnatin tarayya, kungiyoyin addinai da kuma na al'adu akan shimfida tsare-tsare na zaman lafiya tsakanin mabiya addinai a Najeriya
A yayin da bikin kirsimeti na mabiya addinin Kirista ke ci gaba da karatowa, mun samu cewa, wata Mata musulma, ta yiwa zaurawan kiristoci gagarumar hidima domin jin dadin gudanar da bukukuwansu cikin annashuwa a wani yanki na jihar Kaduna.
Wannan Mata, Hajiya Ramatu Tijjani, ta bayar da gudunmuwa da kuma tallafi na kayan abinci da kuma sutura ta Atamfofi ga Mata zaurawa domin gudanar da shagulgulansu na bikin Kirsimeti cikin walwala da kuma jin dadi.
Majiyar Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Hajiya Ramatu ta yi wannan gagarumar bajinta ne da babbar manufa ta kara dankon zumunta da kuma zaman lafiya gami da hadin kai a tsakanin al'umma mabiya addinan biyu a yankunan jihar Kaduna.

Asali: UGC
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Hajiya Ramatu ta bayar da bayar da gudunmuwa ta rarraba kayan abinci da kuma Atamfofi a babban Cocin Church of Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke yankin Sabuwar Tasha a jihar Kaduna.
A yayin zayyana jawabanta, Hajiya Ramatu ta bayyana cewa, wannan kudiri na kyautatawa zai tumfaya har zuwa zuwa wasu manyan Coci dake fadin jihar da kuma na wasu jihohin da ke makwabtaka da jihar Kaduna.
Ya ci gaba da cewa, ta yi wannan hobbasa ne domin inganta jin dadin Zaurawa da kuma 'yan gudun hijira mabiya addinin Kirista da manufa ta habaka dankon zumunci da kuma zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban da ke fadin Najeriya.
KARANTA KUMA: 2019: Goyon baya na Obasanjo ba zai tseratar da Atiku daga rashin nasara ba - Lai Mohammed
Hajiya Ramatu ta kuma yi kira zuwa ga gwamnatin tarayya, kungiyoyin addinai da kuma al'adu wajen samar da hanyoyi da tsare-tsare na wanzar da zaman lafiya da zai kawo karshen rikicin addini da kuma kabilaci.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kungiyar Malaman jami'o'i ta ASUU, za ta ci gaba da gudanar da yajin aikin da ta afka makonni kadan da suka gabata duk da zaman sulhu da gudanar tare da gwamnatin tarayya a jiya Litinin.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng