Yanzu-yanzu: Jigo a jam'iyyar APC da magoya bayansa sun koma PDP a Kebbi

Yanzu-yanzu: Jigo a jam'iyyar APC da magoya bayansa sun koma PDP a Kebbi

Ciyaman din jam'iyyar PDP na jihar Kebbi, Haruna Saidu ya shaidawa duniya cewa tsohon kakakin majalisar jihar, Dan Musa Ribah ya sauya sheka daga APC zuwa PDP sai dai Ribah bai hallarci wajen taron da aka shirya na karbarsa da magoya bayansa ba.

Alhaji Dan Musa Ribah, jigo a jam'iyyar All progressives Congress (APC) a karamar hukumar Danko-Wasagu na jihar Kebbi ya tattara nasa ya nasa tare da dimbin magoya bayansa ya koma jam'iyyar adawa ta PDP.

Daily Trust ta ruwaito cewa ciyaman din jam'iyyar PDP na jihar Kebbi, Alhaji Haruna ne ya fadi hakan a karshen makon da ta gabata a Ribah yayin da ya ke karbar wadanda suka dawo jam'iyyar a wata tattaki da aka shirya a garin Ribah.

Yanzu-yanzu: Jigo na jam'iyyar APC da magoya bayansa sun koma PDP a Kebbi
Yanzu-yanzu: Jigo na jam'iyyar APC da magoya bayansa sun koma PDP a Kebbi
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 2019: Korafin babban sarki a arewa ya kai APC hannun DSS

Ya ce dan Alhaji Dan Musa bai samu ikon hallartar taron da aka shirya domin shi da magoya bayansa ba saboda wasu mutanen da ba a gano ko su wanene ba sunyi awon gaba da shi.

Saidu ya yi bayanin cewar kafin fara bikin karbar sabbin mambobin, tsohon kakakin majalisar jihar ya fada masa cewa ya yanke shawarar ficewa daga APC ne saboda jam'iyyar ba ta masa adalci a yayin da ya ke bukatar taimako.

Ya ce: "Mun hallarci wannan taron ne saboda ya tabbatar min cewa ya fice daga APC ya dawo PDP. Ya umurci magoya bayansa da al'ummar garinsu su koma PDP kuma gashi muna karbarsu a yau."

Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar, Sanata Isah Galaudu ya tabbatarwa sabbin mambobin cewa babu wanda zai nuna musu banbanci a jam'iyyar PDP.

A halin yanzu, majiyar Legit.ng ta ce tana kokarin ji ta bakin Alhaji Dan Musa Ribah domin tabbatar da lamarin ficewarsa a APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164