'Kun riga rana faduwa' - Babban Fasto a kudu ya ci fuskar Obi a gaban jama'a, bidiyo

'Kun riga rana faduwa' - Babban Fasto a kudu ya ci fuskar Obi a gaban jama'a, bidiyo

A wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta na Facebook, an ga Rabaran Mbaka, babban Fasto a yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo, na cin fuskar dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Peter Obi.

A cikin faifan bidiyon, Mbaka ya dafa Obi tare da shaida ma sa cewar takarar su babu inda za ta, tamkar sun fadi zabe ne.

Mbaka ya yi magana ne cikin harshen Igbo, duk da ya kan dan tsarma da Turanci.

Majiyar legit.ng da ke fuskantar yaren Igbo ta tabbatar ma ta da cewar kalaman Mbaka ga Obi cin fuska ne.

Ku kalli faifan bidiyon:

Mbaka ya kasance daga cikin 'yan tsirarun kabilar Igbo da su ka fito fili su ka nemi jama'ar yankin kudu maso gabas su zabi shugaba a zaben shekarar 2015.

'Kun riga rana faduwa' - Babban Fasto a kudu ya ci fuskar Obi a gaban jama'a, bidiyo
Mbaka da Buhari
Asali: Depositphotos

Sai dai a wannan karon, Limamin na darikar Katolika kuma shugaban Adoration Catholic Prayer Ministry da ke Enugu, Reverend Father Ejike Mbaka ya yi hasashen cewa akwai yiwuwar Shugaba Muhammadu Buhari da dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar za su fadi sha kaye a zaben 2019.

Babban malamin addinin ya fadi hakan ne a yayin bikin baje kolin amfanin gona na 2018 a Adoration Ground da ke garin Emene.

DUBA WANNAN: Na albarkaci abinda su ka yi - Gwamnan APC ga wadanda suka fita daga jam'iyyar a jihar sa

Ya yi ikirarin cewa adduo'in da 'yan cocin adoration su kayi ne ya sanya Buhari samun nasarar zama shugaban kasa. Mbaka ya koka kan yadda shugaban kasar ya ki zuwa cocin ya yi wani aiki ko bayar da gudunmawa domin nuna godiyarsa ga Allah.

Ya kuma yi ikirarin cewa addu'o'in mabiya cocinsa ne ya warkar da shugba Buhari daga rashin lafiyar da ta same shi a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel