Ma'aikatan kananan hukumomin Zamfara ne ma fi koma baya a albashi

Ma'aikatan kananan hukumomin Zamfara ne ma fi koma baya a albashi

Rahotan da muka samu daga Vanguard ya ce ma'aikatan kananan hukumomi a jihar Zamfara ne su kafi karbar albashi mafi karanci a Najeriya inda aka ce wasu na karbar N6,000 a duk wata.

Ibrahim Khaleel, shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi na kasa (NULGE) ne ya bayyana hakan a Abuja gabanin bikin cika shekaru 40 da kafa kungiyar.

Khaleel ya ce rashin biyar albashi mafi karanci na N18,000 da gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ne babban dalilin da yasa ya ke kawo cikas ga yunkurin karin mafi karancin albashi zuwa N30,000.

Ma'aikatan kananan hukumomin Zamfara ne ma fi koma baya a albashi

Ma'aikatan kananan hukumomin Zamfara ne ma fi koma baya a albashi
Source: Depositphotos

Khaleel, wanda shine ma'ajin kungiyar kwadago na kasa (NLC) ya ce rashin biyan ma'aikatan jihar Zamfara albashi mai gwabi yana daga cikin abinda ke haifar da tashe-tashen hankula da rashin tsaro a jihar.

DUBA WANNAN: Shugabanin kabilar Yarabawa sun goyi bayan Atiku

Kungiyar kwadagon ta ce muddin ba a biyan ma'aikata albashin da ya dace a biya su, zai yi wahala a samu zaman lafiya a jihar.

Khaleel ya kuma zargi gwamna Simon Lalong na jihar Plateau da rashin biyan ma'aikatan jihar sa albashi mafi karanci na N18,000. Ya ce ma'aikatan kananan hukumomi a jihar suna karbar wani kasho ne kawai daga N18,000.

Ya bayyana cewa ma'aikatan kananan hukumomi suna wadanda suka fi rauni a Najeriya.

A cewarsa, za a inganta yanayin ayyukan ma'aikata ne a jihar idan an bari ma'aikatan kananan hukumomi suna gudanar da ayyukansu yadda ya dace.

A kan batun bai wa kananan hukumomi ikon cin gashin kansu, shugaban ya ce kawo yanzu jihohi 12 ne kawai suka bayyana matsayar su kan batun, guda 9 sun goyi bayan bawa kananan hukumomin iko yayin da uku sun ce ba su amince ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel