An janye magungunan hawan jini daga kasuwa da farmasi, an gano suna sanya cutar kansa

An janye magungunan hawan jini daga kasuwa da farmasi, an gano suna sanya cutar kansa

- Shan wasu magani guda biyu na hawan jini ka iya canyo kamuwa da ciwon cancer

- Duk wani mara lafiya dake shan daya daga cikin su ya gaggauta ziyartar likitansa

- Maganin na dauke da wani sinadari daka iya canjo ciwon cancer

An janye magungunan hawan jini daga kasuwa da farmasi, an gano suka sanya cutar kansa
An janye magungunan hawan jini daga kasuwa da farmasi, an gano suka sanya cutar kansa
Asali: Depositphotos

Wani bincike da Teva Pharmaceuticals ta fitar ya bayyana cewa akwai wasu magungunan hawan jini guda Biyu da shansu yana iya janyo kamuwa da ciwon cancer.

A wani bayani da Teva ta turawa FDA tace hada wadannan magunguna biyu masu suna Amlodipine da kuma valsartan yanada matukar illa.

Magungunan suna dauke da wani sinadari mai suna N-nitroso-diethylamine(NDEA) wanda wannan sinadari yana iya janyo kamuwa da cutar Kansa.

DUBA WANNAN: Ko kunsan nawa jihar Kano ke kashewa kan albashi kadai a kowanne wata?

Duk wani mara lafiya da yake shan daya daga cikin wadannan magungunan biyu to ya gaggauta ziyartatar likitansa don neman shawara da bincike.

Sannan dakatar da shan maganin ba tare da wani bincike ba ka iya jefa mara lafiyar cikin hatsari.cewar Teva.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel