Na yi aikin yaron mota kafin in zama Gwamna – Samuel Ortom

Na yi aikin yaron mota kafin in zama Gwamna – Samuel Ortom

- Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya bada labarin yadda ya taba zama yaron mota

- Samuel Ortom yace idan Ubangiji yayi nufin mutum da nasara, idan har ya dage sai ya kai

- Direbobin Jihar sun kai wa Gwamnan ziyara kwanan nan inda su ka nuna goyon bayan su

Na yi aikin yaron mota kafin in zama Gwamna – Samuel Ortom
Gwamna Benuwai Ortom yayi aikin karen mota shekaru 45 da su ka wuce
Asali: Depositphotos

Mai Girma Gwamna Samuel Ortom ya bada labarin yadda ya soma aikin karen mota a shekarun baya a lokacin da ya fita daga Makarantar Boko. Gwamnan ya bayyana wannan ne a jiya Ranar Alhamis 29 ga Watan Nuwamba.

Samuel Ortom ya fadawa Direbobin keke-napep yadda ya taba yi wa masu motoci yaron mota watau ‘agbero’. Sai dai yanzu Ubangiji ya nufa har ya zama Gwamna mai iko wanda kuma yake neman zarcewa a kan karagar mulki.

KU KARANTA: Gwamna Okorocha zai bijirewa Jam’iyyar APC ya kama DPP a zaben 2019

Gwamnan ya bayyana cewa idan arziki yayi nufin samun mutum, babu abin da zai hana har sai idan ya buge da shaye-shaye da sauran hanyar banza. Ortom yace yayi aikin tukin mota ne a 1972 bayan ya bar karatun Boko a lokacin.

Ortom ya nuna cewa yana alfahari da halin da ya samu kan sa a wancan lokaci bayan karatu ya gagare sa don haka yake fadawa jama’an da su ka ziyarce sa, su kama aikin kirki a maimakon su shiga shaye-shaye da shan mugayen kwayoyi.

Direbobin na keke-napep dai sun jaddadawa Gwamnan cewa su na tare da shi a zabe mai zuwa na 2019 saboda irin kokarin da yayi a kan mulki. Ortom dai ya sauya sheka daga APC zuwa Jam'iyyar PDP kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel