Ba bu wata kitimurmura ta tsige Gwamna Emmanuel - APC

Ba bu wata kitimurmura ta tsige Gwamna Emmanuel - APC

- Jam'iyyar mai ci ta APC ta musanta rashin duk wani tuggu na tsige Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom

- Jam'iyyar ta bayyana cewa ba bu wani dalili da zai sanya a tsige gwamnan da wa'adin zaman bisa Kujerarsa bai wuci watanni uku ba

- Jam'iyyar ta kuma bayyana amincinta ga sabon Kwamshinan 'Yan sanda na jihar

A jiya Alhamis jam'iyya mai ci ta APC ta bayyana cewa, ba ta da wani shiri na tsige gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom daga kan kujerar sa sabanin yadda ake ikirari dangane da rikicin siyasa ya yi kaka gida a fadin jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, shugaban jam'iyyar APC na jihar Kwara, Ime Okopido, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai a farfajiyar majalisar dokoki ta jihar.

Rahoton kamar yadda Okopido ya ruwaito ya bayyana cewa, jam'iyyar APC da kuma majalisar dokoki ba za su ribaci lokacin su ba wajen fara wani shirye-shirye na tsige gwamnan da wa'adinsa bisa kujerar bai wuci watanni uku ba.

Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom

Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom
Source: Depositphotos

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Okodipo ya bayyana hakan ne yayin mayar da martani ga furucin ranar 27 ga watan Nuwamba na shugaban jam'iyyar PDP jiha, Paul Ekpo da ya bayyana cewa 'yan majalisar dokokin na jihar da ke karkashin jam'iyyar APC sun fara aiwatar da shirye-shirye na tsige gwamna daga kujerar sa.

KARANTA KUMA: Najeriya ta shigo Litar Man fetur 4.37bn cikin watanni 3 kacal - NBS

Mista Okodipo ya bayyana cewa, ko shakka ba bu wannan kagaggen zance ne mara tushe ko madogara da 'yan adawa suka assasa da manufa ta yaudarar al'umma.

Kazalika jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsohon shugaba maras rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya musanta zargin sa hannunsa cikin dambarwar siyasa da ta auku cikin majalisar dokoki ta jihar a ranar Talatar da ta gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel