Sake Zaben Buhari zai inganta Dimokuradiyya a Gwamnatin Najeriya - Jigon APC

Sake Zaben Buhari zai inganta Dimokuradiyya a Gwamnatin Najeriya - Jigon APC

Alhaji Mu'azu Bawa, wani jigon na jam'iyya ia ci ta APC reshen jihar Neja, ya bayyana cewa sake zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 zai tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya a gwamnatin kasar nan.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Alhajin Bawa ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa a cikin birnin Minna a yau Alhamis.

Ya ke cewa, ba bu wani mafificin dan takarar kujerar shugaban kasa mai nagarta cikin manema takarar shugaban kasa a zaben 2019 da ya wuce shugaba Buhari da ko shakka ba bu zai tabbatar da kwararar bukatu da cika burikan al'ummar kasar nan.

Alhaji Bawa ya kuma yi kira ga fusatattun mambobin jam'iyyar ta APC da su yayyafawa zukatan su ruwan sanyi da zai tabbatar da hadin kai da karfafuwa ta jam'iyyar wajen cimma nasara yayin babban zaben kasa na badi.

Sake Zaben Buhari zai inganta Dimokuradiyya a Gwamnatin Najeriya - Jigon APC

Sake Zaben Buhari zai inganta Dimokuradiyya a Gwamnatin Najeriya - Jigon APC
Source: Depositphotos

Jigon na APC ya kara da cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta zayyana sadaukarwar ta da kuma dukufa gami da jajircewa baya ga tsayuwar daka wajen sauke nauyin al'ummar kasar nan da rataya a wuyanta musamman ta fuskar shimfida muhimman aikace-aikace na ci gaba.

KARANTA KUMA: Ana sa ran cutar Kanjamau za ta kassara Matasa 360,000 zuwa shekarar 2030 - UNICEF

Ginshikin na jam'iyyar APC da ya kasance tsohon kwamishinan Kudi na jihar Neja, ya kuma kyautata zaton sa gami da sa rai akan shugaba Buhari wajen tabbatar da al'ummar kasar nan sun sharbi romon dimokuradiyya yayin da ya cimma nasara a zaben kasa na 2019.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a yau shugaban kasa Buhari ya shilla zuwa kasar Chadi domin ganawa da shugabannin kasashen biyar na nahiyyar Afirka dangane da ruruma da sake kunno kai na ta'addancin mayakan Boko Haram.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel