Zainab Husaini: Dalibar da wasu masu garkuwa da mutane suka sace a Katsina

Zainab Husaini: Dalibar da wasu masu garkuwa da mutane suka sace a Katsina

Wani rahoto da muka samu da dumi dumi shine wasu gungun yan bindiga da ba’a san daga inda suka fito ba sun kai wani samame cikin karamar hukumar Dutsanma ta jahar Katsina, inda suka yi awon gaba da wata budurwa mai suna Zainab Hussaini.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Binisanusi Sakkwato ne ya bayyana haka a shafinsa a ranar Laraba 28 ga watan Nuwamba, inda yace masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da Zainab ne daga gidan kakanta dake garin Maitsani.

KU KARANTA: Tsananin matsin rayuwa ta kai wani ma’aikacin gwamnati ga rataye kansa da kansa har lahira

Zainab Husaini: Dalibar da wasu masu garkuwa da mutane suka sace a Katsina

Zainab Husaini
Source: UGC

Majiyar Legit.com ta bayyana cewa Zainab dalibar ilimi ce a makarantar koyon aikin asibiti dake garin Dutsanma, inda take karantar ilimin kula da hakori, kuma a yanzu haka take neman kwarewa da sanin makaman aiki a sashin kula da hakori na babban asibitin garin Dutsanma.

Wannan lamari na satar Malama Zainab ya faru ne bayan kimanin sati biyu ko uku da wasu gungun yan bindiga suka sako wasu yan tagwayen mata Hassana da Hussaina a jahar Zamfara, bayan kwashe sama da wata guda a hannu.

Su dai wadannan yan mata sun fada hannun masu garkuwan ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa rabon katin aurensu da za’a bada jimawa ba, inda yan bindigan suka nemi a biyasu kimanin miliyan dari a matsayin kudin fansa, amma daga bisani suka rage.

Da kyaru da sudin goshi aka hada miliyoyin da miyagun suka nema, inda har sai da Sanata Zamfara ta tsakiya, Kabiru Marafa ya taimaka ma iyayenta da kudi naira miliyan shida a kokarinsu na harhada kudaden.

Fatanmu anan shine Allah ubangijin kowa da komai, mai iko akan komai da kowa ya kubutar da Zainab Hussani daga hannun miyagun mutanen da suka yi garkuwa da ita, kuma Allah ya tona asirinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel