Boko Haram: APC ta zargi PDP da siyasantar da kisan sojojin Najeriya

Boko Haram: APC ta zargi PDP da siyasantar da kisan sojojin Najeriya

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta zargi jam'iyyar adawa ta Peoples’ Democratic Party (PDP) da amfani da kissar kiyashin da 'yan Boko Haram suka yiwa sojojin Najeriya a sasaninsu da ke Metele wajen cimma manufar siyasa.

Babban sakataren yada labarai na kasa na APC, Malam Lanre Issa-Onilu ne ya yi wannan zargin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja.

Issa-Onilu ya ce PDP tana shirin amfani da iftila'in da ya faru domin cimma manufar siyasa.

Boko Haram: APC ta zargi PDP da siyasantar da kisan sojojin Najeriya
Boko Haram: APC ta zargi PDP da siyasantar da kisan sojojin Najeriya
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Gwamna Yari ya dakatar da sarakuna hudu a Zamfara

"Bisa ga dukkan alamu jam'iyyar PDP da dan takarar shugabancin kasar ta, Alhaji Atiku Abubakar sun yanke shawarar cin mutuncin jaruman sojojin mu da suka rasu a harin da Boko Haram ta kai sansanin soji da ke Metele a kwanan nan.

"Jam'iyyar PDP da Atiku suna amfani da rasuwar sojojin mu domin cimma manufar siyasa.

"Abinda su keyi cin mutunci ne ga iyalan sojojin da daukakin hukumar sojojin Najeriya da ke aiki dare da rana domin kiyaye iyakar kasarmu.

"Yan Najeriya sun gano wannan mummunan dabarar ta PDP kuma za su mayar da martani idan zabe ya zo," inji Kakakin na jam'iyyar APC.

Ya yi ta'aziyyar rasuwar sojojin da suka mutu da ma dukkan wasu jami'an tsaro da suka mutu a bakin aiki.

Issa-Onilu ya bukaci sojojin su mayar da hankali kan muhimmin aikin da ke gabansu da samar da tsaro ga kasarmu Najeriya.

Kakakin na jam'iyyar APC ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tana iya kokarinta domin ganin ta kawo dawamamen zaman lafiya a dukkan sassan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164