Ka bani umarni na shiga dajin Sambisa na halaka yan Boko Haram – Gudaji Kazaure ga Buhari
Dan majalisan wakilan Najeriya, dake wakiltar al’ummar Kazaure, Roni da Yan kwashi ya dauki alwashin shiga dajin Sambisa tare da halaka duk wasu mayakan Boko Haram daya tarar a cikin dajin cikin dan kankanin lokaci.
Legit.com ta ruwaito Gudaji Kazaure ya bayyana haka ne cikin wata bidiyo dake yawo, inda yace fatansa kawai a yanzu shine shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi umarnin shiga dajin Sambisa, tare da dakarun Sojoji da jami’an Yansanda, da kuma bindiga.
KU KARANTA: Katankatana: Wani Mutum ya bude wuta a kotu, ya kashe matarsa da surukinsa
Da aka tabmbayeshi ko dame yake tinkahon tarar abinda ko Sojoji ma ya suka kare dashi, sai yace ai shi mafarauci ne, don haka ya saba shiga dokar daji yayi farauta, hakan ne ma yasa ya san sirrin farauta a cikin daji, don haka wannan ba wani bane mai wuya a gareshi.
“Shugaban kasa ya bani umarni ya gani, zan jagoranci tawagar mafarauta ta musamman zuwa cikin dajin nan mu gama da yan iskan nan cikin ruwan sanyi, ni fa mafarauci ne, don haka na san duka dazukan nan, zan tura tawagar mafarauta ta musamman.
“Abinda nakeso kawai shine gwamnati ta bamu dakarun Soji da jami’an Yansanda, mu kuma zamu shiga cikin dajin, na fada muku ni ne zan jagoranci tawagar nan zan jagaoranci tafiyar, ko da gobe ne kuwa.” Inji shi.
Wannan magana ta dan majalisa Gudaji ta biyo bayan sake farfadowar ayyukan mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas ne, inda a yan kwanakin da suka gabata aka ruwaito yan ta’addan sun tafka ma dakarun Sojin Najeriya babbar asara.
Haka zalika hare haren da suke kaiwa kauyukan gefen garin Maiduguri sun karu matuka, inda suka tashi kauyuka da dama daga aiki, tare da kona gidajensu, kwashe kayan abincinsu, kashe mutanen garin da kuma yin garkuwa da wasunsu musamman mata.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng