Buhari ya nada Kabiru Bala a matsayin jakadan Najeriya a Afrika ta Kudu

Buhari ya nada Kabiru Bala a matsayin jakadan Najeriya a Afrika ta Kudu

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Kabiru Bala a matsayin jakadan Najeriya a kasar Africa ta Kudu da kuma kasashen Swaziland da Lesotho.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun ministan harkokin kasashen waje, Sarah Sanda, Mr Bala ya karbi takardun kama aikinsa daga ministan harkokin kasa waje Geoffrey Onyeama.

Kafin yi masa wannan nadin, Mr Bala ya kasance shine mataimakin jakadan Najeriya a kasar Ingila.

Buhari ya nada Kabiru Bala a matsayin jakadan Najeriya a Afrika ta Kudu
Buhari ya nada Kabiru Bala a matsayin jakadan Najeriya a Afrika ta Kudu
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Gwamna Ganduje ya bawa hukumomin yaki da cin hanci gudunmawar miliyoyi

Ya fara aiki ne a ma'aikatar harkokin kasashen waje a shekarar 1999 kuma ya yi aiki a Brasilia, Sudan, Gambia, Nethelands da Thailand.

Ya kuma yi aiki a sassa daban-daban a ma'aikatan na harkokin kasashen waje da kuma fadan shugaban kasa da kuma ofishin babban mai tsaron shugaban kasa.

An bakaci ya tabbatar da cewa ya inganta dangata mai kyau tsakanin Najeriya ta Afrika ta Kudu.

An nada Mr Bala a matsayin jakadar Najeriya a Afrika ta kudu ne sakamakon murabus da Ahmed Ibeto ya yi bayan ya fice daga jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress, APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164