Jiragen dankaro guda 32 sun nufo Najeriya dauke da man fetir da kayan masarufi

Jiragen dankaro guda 32 sun nufo Najeriya dauke da man fetir da kayan masarufi

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA, ta bayyana cewa suna tsimayin isowar manyan jiragen ruwa guda Talatin da biyu zasu isa tashoshin jiragen ruwan Najeriya nan bada jimawa ba, inji rahoton kamfanin dillancin labaru,NAN.

Majiyar Legit.com ta ruwaito hukumar NPA tace tana sa ran jiragen zasu fara isowa Najeriya ne daga ranar Litinin 26 ga watan Nuwamba zuwa 30 ga watan Nuwamba, muma suna dauke ne da tataccen man fetir da kayan abinci.

KU KARANTA: Ba rabo da gwani ba: Muhimman abubuwa 12 game da marigayi Abba Kyari

Hukumar NPA ta kara da cewa jiragen zasu sauke kayan da suka yi dako ne a tashar jirgin ruwa na Apapa da na Tin Can, inda tace jirage 12 daga cikin 32 na dauke tataccen man fetir, yayin da sauran jirage 20 ke dakon kifi, fulawa, man jirgin sama da dai tarkacen kayayyaki daban daban.

Jiragen dankaro guda 32 sun nufo Najeriya dauke da man fetir da kayan masarufi
Jirgin dankaro
Asali: UGC

Kamar yadda hukumar ta tabbatar a cikin sanarwar data fitar a ranar Litinin cewa a yanzu haka akwai jiragen ruwa guda goma sha biyu suna jiran umarnin sauke kayan da suka dauko da suka hada da takin zamani, mai da sundukai da dama.

A kusan kullum ana samu jirage akalla guda biyar dake shigowa Najeriya domin sauke kayayyakin da yan kasuwa suka sayo daga kasashen wajen, domin kuwa ko a watan Oktobar data gabata sai da wasu jirage ashirin da biyu suka shigo da kaya Najeriya.

Jiragen sun yi jigilar kayan ne daga ranar 2 ga watan Oktoba zuwa 27 ga watan Oktoba, inda suka shigo da kayayyakin abinci da man fetir, kamar yadda hukumar NPA ta tabbatar.

NPA tace jirage takwas daga cikin gua ashirin da bakwai na dauke da tataccen man fetir, yayin da sauran jirage goma sha tara ke dauke da fulawa, Siga, kayan gine gine, da ma sauran kayayyaki da dama.

Sai dai a wancan karo hukumar ta tura jirage guda goma zuwa tashar jirgin ruwa dake garin Calabar na jahar Cross Rivers, inda suka sauke man fetir.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel