Fashola ya kai ziyarar gani da ido zuwa wani muhimmin aiki da Buhari ke yi a Kaduna
Dangane da kokarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi na ganin an samar da isashshen wutar lantarki a Najeriya gaba daya, ministan ayyuka, gidaje da lantarki, Babatunde Fashola ya kai ziyarar gani da ido zuwa wata cibiyar samar da wutar lantarki dake jahar Kaduna.
Legit.com ta ruwaito Fashola ya isa wannan cibiyar samar da wutar lantarkin dake unguwar Kudenda ne da misalin karfe 6 na yamma, inda ya dan kwangilan dake gudanar da aikin gina cibiyar Injiniya Sunny Okwedi ya zazzagaya da shi.
KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: Tsohon gwamnan Kaduna Abba Kyari ya rasu

Source: UGC
Injiya Sunny ya tabbatar ma minister Fashola cewa a yanzu haka na’urorin kulawa da wutar lantarkin sun iso, da ma sauran kayayyakin da suke bukata, a yanzu haka yace suna aikin dasa na’urorin ba tare da wata matsala ba.
Injiniya Sunny ya kara da cewa a yanzu haka sun kammala duk wani aikin Injiniyoyi da kasha 98, sun kammala sayan duk kayan aikin da ake bukata da kasha 93, haka zalika sun kammala duk wani aikin gine gine a cibiyar da kasha 76.
A nasa jawabin, Minista Fashola ya bayyana cewa ya isa jahar Kaduna ne don tattaunawa da wasu jami’an hanya, amma sai yaga dacewar ya leka wannan aikin samar da wutar lantarki na mega wata 215 don gane ma idanunsa aikin da ake yi.

Source: UGC
“Duk da yake ina samun rahoton aikin a duk wata, da kuma cigaban da ake samu, amma naga dacewar tunda dai na shiga garin Kaduna, ya kamata na leka cibiyar don game ma idanuwana aikin da ake yi. A gaskiya na gamsu da aikin da ake yi.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng