An sami matsala a PDP a Kwara: Saraki ya sa gwamnansa ya fasa takara
- Bokula Saraki ya nemi gwamna Abdulfatah daya ajjiye takarar sa
- Ahmed yace Saraki ya nemi ya janye ne biyo bayan wani karamin hargitsi da akayi da PDP a zaben daya gudana a jihar tasa
- Gwamnan yace janyewar tasa ba abinda zai tsinanawa jam'iyar

Asali: Depositphotos
A ranar 24 ga watan Nuwamba gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed ya bayyana cewa an nemi ya janye daga takarar da yake nema ta sanata ya barwa Abdulrafi'u Ibrahim.
Rahoton ya bayyana cewa wannan batu na bukatar janyewar tasa ya fito ne daga bakin Bukola Saraki.
DUBA WANNAN: Yawan yara da basu zuwa makaranta a Najeriya
Kasancewar Saraki shugaban jam'iyar kuma yafi ra'ayin Abdulrafi'u yaci gaba da zama akan kujerar sa ya nemi gwamnoni da dama dasu sarayar masa da takarar su.
Gwamnan ta bakin babban mataimakin sa akan harkar labarai yace janyewar tashi daga neman kujerar sanata ba abinda zata amfani jam'iyar dashi.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng