Dakarun soji sun samu nasara a kan gagararrun makiyayan Benuwe

Dakarun soji sun samu nasara a kan gagararrun makiyayan Benuwe

Hedkwatar hukumar tsaro ta kasa ta bayyana cewar yanzu haka dukkan jama'ar da rikicin makiyaya ya shafa a jihar Benuwe sun koma gidajensu bayan ganin bayan 'yan ta'addar makiyaya da su ka addabi sassan jihar.

John Agim, darektan yada labaran hukumar tsaro, ne ya sanar da haka a yau, Asabar, tare da sanar da cewar atisayen soji ne ya kawo karshen aiyukan ta'addanci na makiyayan.

A cewar sa, jami'an soji sun rushe duk wani sansanin makiyaya da ke fadin jihar ta Benuwe.

Dakarun soji sun samu nasara a kan gagararrun makiyayan Benuwe
Dakarun soji sun samu nasara a kan gagararrun makiyayan Benuwe
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya yi magana a kan kisan sojojin Najeriya 118

Agim ya kara da cewar nasarar da atisayen dakarun soji ya samu bai tsaya iya jihar Benuwe, ya shiga har jihohin Nasarawa da Taraba, da ke makwabtaka da jihar Benuwe.

A cewar sa, babu wani sansanin makiyaya da ya rage a jihar Benuwe kuma tuni jama'ar da su ka gudu sun koma garuruwansu na kakanni da iyaye.

Kazalika, Agim ya ce dakarun soji sun yi nasarar rage aiyukan ta'addanci na kungiyoyin 'yan bindiga daban-daban da ke jihar Benuwe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng