Na dukufa domin tabbatar da zabe na gaskiya da adalci - Shugaba Buhari ga 'Yan Najeriya
Mun samu cewa a yau Asabar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake jaddada matsayarsa ta dukufa wajen tabbatar da an gudanar da zabe na mafi kololuwar gaskiya da kuma adalci a yayin babban zaben kasa da zai gudana a shekarar 2019.
Shugaban Kasa Buhari ya sake jaddada wannan matsaya cikin Birnin Jos na jihar Filato yayin halartar bikin yaye manyan dalibai daga cibiyar horas da tsare-tsare da dabaru ta National Institute for Policy and Strategic Studies da ke garin KURU.
A cewar shugaban kasa, mafificin nauyi da ke gwamnatin sa a halin yanzu bai wuci tabbatar da an gudanar da tsaftataccen zabe na gaskiya da adalci cikin tsare-tsarenta na dukufa wajen tabbatar da kwararar romo na Dimokuradiyya.

Asali: UGC
Shugaba Buhari ya kuma nemi al'ummar kasar nan akan sauke nauyin da rataya a wuyansu na kishin kasa da ya farlanta a gare su kasancewarsa masu ruwa da tsaki na ci gaban kasa.
Ministan tsaro, Birgediya Janar Mansur Dan Ali, shine ya wakilci shugaban kasa Buhari a wannan taro, inda ya bayyana cewa gwamnatinsu ta dukufa wajen tabbatar da ingantaccen shugabanci kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.
KARANTA KUMA: Zan yi ritaya daga Siyasa a 2023 - Sanata Orji
Kazalika shugaban kasar ya bayyana yadda gwamnatinsa ta assasa tsare-tsare da manufofin kawo ci gaba a kasar nan domin fidda ita zuwa ga tudun tsira sakamakon yanayin da ta tsinceta na mawuyacin hali.
A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya Juma'a shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da Ministan tsaro zuwa ga shugaban kasar Chadi, Idris Derby, domin halartar taron tsaro na gaggawa kan tabarbarewar tsaro da ke ci gaba da fantsama kan iyakar kasashen biyu.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng