Mawaki ya kira babban limamin Najeriya da cewa yana cikin kungyar asiri ta duniya
- Da alama dai Daddy Freeze ba zai sakarwa Fastocin Najeriya mara ba
- Ya fara ne daga sukar karbar tilastaccen kudi zuwa sadaka
- Yanzu kuma wai 'yan kungiyar asiri ne suke fake wa da Yesu

Asali: UGC
Sanannen mashiryin shirin gidan rediyo, Daddy Freeze, ba zai sakarwa Fastocin Najeriya mara ba. Ya fara ne da sukar tilastaccen kudi zuwa sadaka da suke karba. Yanzu abun ya kai ga zargin su da kungiyar asiri.
A ranar Alhamis, 22 ga watan Nuwamba ne Daddy Freeze ya yayi rubutu a shafin shi na instagram akan wanda ya samar da jami'ar Winners Chapel and Covenant, Bishop David Oyedepo, a matsayin mai bautar shaidan.
Ya kawo dalilin shi ne hade da hoton mai dauke da sanannun mutane da sukayi alamar mai kusurwa uku da hannayen su.
Wadannan mutanen sun hada da shugaban kasar Amurka Donald Trump, Michelle Obama, Angela Merkel, Steve Harvey, Bishop Oyedepo da sauransu.
DUBA WANNAN: Atiku ya wahal da Obasanjo da cin hancinsa
Daddy Freeze bai tsaya a nan ba har sai da ya kara da hoton jami'ar Covenant wanda aka dauka ta sama, inda ya nuna wani guri da aka zagaye wani zanen tauraruwa da jan fenti, tauraruwa David, wacce alama ce ta addinin Yahudanci.
Ya kara da hoton ma'anar bautar shaidan, wanda tauraruwar David alama ce ta hakan.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng