Kabilanci ko addini ba zai hana ni yaki da cin hanci ba - Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba zaiyi wata-wata ba wajen hukunta duk wani ma'aikacin gwamnati da aka samu da laifin sace dukiyar al'umma ba tare da la'akari da addini ko kabila ba.
Shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a ranar Juma'a yayin da ya karbi tawagar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga jihar Benue karkashin jagorancin Sanata George Akume a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Asali: UGC
Ya ce: "Ban san yadda mutane ke iya barci ba idan ba a biya ma'aikata albashinsu ba. Ma'aikatan suna da hidimomin da za suyi da kudi kamar biyan kudaden makarantar yara, biyan kudin haya, siyan abinci, biyan kudin makaranta da kula da lafiya.
DUBA WANNAN: An kashe kuku bisa zarginsa da sata a gidan gwamna Dankwambo
"Ina tabbatar muku da cewa bana fifita wani bangare na kasar nan fiye da wani.
"Saboda haka, idan wani yana son ya gane cewa bana nuna banbancin kabila ko addini, ya yi sakaci a kama shi dumu-dumu yana satar kudin al'umma. Zanyi maganinsa ko shi wanene."
Shugaban kasan ya fadawa tawagar cewa majalisar zartarwa na tarayya tana sanya idanu kan halin da 'yan Najeriya ke ciki kuma tana duba yadda ake kashe kudin Paris Club da gwamnatin tarayya ta bawa wasu jihohi.
"Ina muku godiya bisa ziyarar da kuka kawo min. Ziyarar ta kara mana kwarin gwiwa," inji shi.
Ya ce gwamnatinsa ta samu nasarori sosai a bangaren inganta tattalin arziki ta hanyar saka jari a harkar noma da kuma tallafawa mutane su kama sana'oi da noma.
Asali: Legit.ng