Me ya hado Amaechi rigima da tsohon abokinsa Sanata Dino Melaye?
- Dino Malaye da Rotimi Amaechi sun kara akan yiyuwar komawar Buhari shugabanci
- Amaechi yana ganin chanchantar Shugaban komawa kan mulki
- Inda Malaye yake ganin sam bai kamata shugaban ya koma kan kujerar ba

Asali: UGC
Sanatan da yake wakiltar jihar Kogi Dino Malaye sun samu sabanin ra'ayi tsakanin shi da Rotimi Amaechi akan yiyuwar komawar Shugaban kasa Muhammad Buhari kan mulki a shekara ta 2019.
A hannu daya Malaye baya ganin Buhari ya cancanta ya koma kan kujerar shugabancin kasar nan a shekara ta 2019.
Yayin shi kuwa Amaechi yake ganin babu wanda yafi kamata ya kara komawa kan kujerar kamar Muhammad Buhari.
A lokacin da ake gudanar da wannan tattaunawa a Osasu Symposium a ranar 22 ga watan Nuwamba a Abuja Malaye yace a wannan gwamnati ne aka samu tsaiko wajen fitar da kasafin wannan kasa.
DUBA WANNAN: Lokacin karin albashi yayi - CBN
Amaechi yace Buhari yana sanya hannu ne akan duk wani abu saboda yan Najeriya, idan kuma yaki sanyawa to shima saboda yan kasar yayi.
Da Malaye yake maida amsa yace yan Najeriya sunsan Buhari bazai koma kan kujerar sa ba a shekara ta 2019.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng