Abin ya qular da Jonathan: Anqi sayen Littafinsa, amma ana ta karantawa a wayoyi

Abin ya qular da Jonathan: Anqi sayen Littafinsa, amma ana ta karantawa a wayoyi

- Jonathan yayi magana akan littafin sa da ake yadawa wanda ya kasance jabu

- Ya saki littafin ne a ranar zagayowar haihuwar sa

- Zaku banbance littafin ne ta hanyar bangon su

Abin ya qular da Jonathan: Anqi sayen Littafinsa, amma ana ta karantawa a wayoyi
Abin ya qular da Jonathan: Anqi sayen Littafinsa, amma ana ta karantawa a wayoyi
Asali: UGC

Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi magana akan littafin sa da wasu suke yadawa wanda ya kasance bogi, maimakon a sayi wanda ya fitar a wannan makon.

Jonathan ya fitar da littafin nasa mai suna "My Transition Hours" a ranar zagayowar haihuwar sa inda ya cika shekara 61 a duniya.

Abin ya qular da Jonathan: Anqi sayen Littafinsa, amma ana ta karantawa a wayoyi
Abin ya qular da Jonathan: Anqi sayen Littafinsa, amma ana ta karantawa a wayoyi
Asali: Twitter

A ranar Alhamis Jonathan ya sanya a shafinsa na twitterinda yake cewa "an samu wasu bata gari suna yada littafi na dana fitar wanda ya kasance ba na gaskiya bane".

"Mutane su rabu da wannan littafi da ake yadawa a kafafen sada zumunta, saboda abubuwan dake ciki ba daya bane da abinda yake cikin littafin da na fitar kwanaki biyu da suka gabata a Abuja." Sanarwar tace.

DUBA WANNAN: An tona Atiku a matsayin mahandami a gwamnati

Sannan daga karshe ya bayyana wasu hanyoyi da mutane zasu gane na gaskiya da na jabu.

Abin ya dai bashi haushi inji majiyarmu, ganin littafin da ake yadawa, dama kalaman da ake cewa nashi ne, sam ba haka suke ba cikin littafin.Ana sai da littafin ne daga N5000 har zuwa N20,000 a yanzu haka a Najeriya.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng