Ra'ayin 'yan Najeriya a kan alkawuran Atiku
A ranar Litinin, 19 ga watan Nuwamba, ne Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya kaddamar da manufofinsa na yakin zabe.
Daga cikin alkawuran da Atiku ya dauka akwai batun inganta tattalin arzikin kasa da zai kai ga tsamo 'yan Najeriya miliyan 50 daga kangin matsin tattalin arziki cikin shekaru biyu kacal.
Atiku ya bayyana cewar ya samu kwarewa a bangaren samar wa matasa aikin yi saboda ya taso matsayin maraya da sai ya sayar da itace kafin ya samu kudin daukar nauyin karatunsa. Sannan ya kara da cewar yanzu lokaci ya yi da zai biya Najeriya halaccin da ta yi ma sa a baya.
Sai dai 'yan Najeriya da ke bin shafin Atiku a Tuwita sun bayyana mabanbantan ra'ayi a kan alkawura da manufofin kamfen din Atiku.

Asali: Facebook
Yayin da wasu su ka bayyana cewar sun gamsu da alkawuran na Atiku, wasu cewa su ke duk yaudara ce irin ta 'yan siyasa, musamman lokacin da su ke yakin neman zabe.
Masana tattalin arziki sun nuna shakku a kan manufar Atiku ta ikirarin cewar zai tsamo 'yan Najeriya da yawansu zai kai mutum miliyan 200 daga talauci cikin shekaru biyu, musamman idan aka yi la'akari da karancin kayan more rayuwa da Najeriya ke fama da shi.
DUBA WANNAN: Bikin mauludi: Babban Sarki a arewa ya nemi jama'a su goyawa Buhari baya
"Akwai banbancin tsakanin karfin tattalin arziki da tsamo mutane daga mutane daga talauci. Samawa jama'a muhalli da gida da abinci ba shine ma'anar raba jama'a da talauci ba," a cewar masanin tattalin arziki, Mohammed Al-Salafi.
Tun bayan da Atiku ya kaddamar da manufofinsa na yakin neman zabe, masana ke cigaba da yin tsifa da hasashen iya cika alkawuran da Atiku ya dauka.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng