Danyen hukunci: Miji ya datse hannun matarsa bayan ya rasa N13,000 da ya ajiye a gida

Danyen hukunci: Miji ya datse hannun matarsa bayan ya rasa N13,000 da ya ajiye a gida

Wata ktoun Majistare da ke zamanta a Iyaganku a Ibadan ta bayar da umurnin a bawa wani magidanci mai shekaru 50 a duniya, Olusola Ojewole masauki a gidan yari bisa zarginsa da datsewa matarsa hannu da adda.

Shugaban kotun, Mr Abdulateef Adebisi ya ce wanda ake zargin sai cigaba da zama a gidan yarin har sai lokacin da za a saurari shari'arsa a ranar 27 ga watan Disamban shekarar 2018.

Adebisi bai ji ta bakin wanda ake zargin ba a yanzu.

Ana tuhumar Ojewole da ke zaune a Iyana Apapa, Moniya a Ibadan da laifin yunkurin kashe matarsa.

Danyen hukunci: Miji ya datse hannun matarsa bayan ya rasa N13,000 da ya ajiye a gida
Danyen hukunci: Miji ya datse hannun matarsa bayan ya rasa N13,000 da ya ajiye a gida
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Magu ya nemi a dena kai shari'ar EFCC gaban wata alkaliya

Mai shigar da kara, Saja Opeyemi Olagunji ya shaidawa kotu cewa a ranar 4 ga watan Nuwamba misalin 12 na rana wanda ake zargin ya yi yunkurin kashe Dorcas Olusegun ta hanyar sarar ta da adda a hannu.

"Ojewole ya yi ikirarin cewa Dorcas ta sace masa N13,000 da ya ajiye a dakinsa amma ta musanta cewa ta dauki kudin.

"Lamarin ya janyo anyi musayar naushi tsakanin mata da mijin wadda hakan yasa Dorcas ta tafi dakin wata makwabciyarta.

"Tayi tsamanin wanda ake zargin ya fita daga gida ne amma tana bude kofar gidan makwabciyarta sai ya kai mata sara da adda a hannunta," inji Olagunji.

Ya ce daga bisani an gano kudin a dakin ma'auratan.

A cewar dan sandan mai shigar da kara, laifin ya sabawa sashi na 320 na Criminal Code Cap 38, Vol II na jihar Oyo na shekarar 2000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164