Ku fatattaki Buhari daga fadar Shugaban Kasa - Atiku ga Magoya Bayansa a Jihar Adamawa

Ku fatattaki Buhari daga fadar Shugaban Kasa - Atiku ga Magoya Bayansa a Jihar Adamawa

Mun samu cewa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya nemi magoya bayansa akan fatattakar shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkanin makarrabansa na gwamnatin tarayya daga kujerar shugabancin kasar nan.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, tsohon mataimakin shugaban kasar ya shaidawa magoya bayansa cewa ba bu abinda gwamnatin shugaba Buhari ta haifar face jefa kasar nan cikin kangi na tagayyara.

Atiku ya bayyana hakan ne a mahaifarsa ta jihar Adamawa yayin halartar wani shiri da kungiyar Matasa magoyan bayansa suka dauki nauyin gudanarwa da ta ke neman ya kara zage dantsensa gami da jajircewa wajen lallasa shugaba Buhari a babban zabe na 2019.

Ku fatattaki Buhari daga fadar Shugaban Kasa - Atiku ga Magoya Bayansa a Jihar Adamawa
Ku fatattaki Buhari daga fadar Shugaban Kasa - Atiku ga Magoya Bayansa a Jihar Adamawa
Asali: Depositphotos

Turakin na Adamawa wanda ya halarci taron da aka gudanar a Silima ta Lamido da ke garin Jimeta a daren ranar Larabar da ta gabata, ya bayyana cewa Buhari ya gaza ta fuskoki daban-daban na jagoranci da ba bu wata sauran dama da ta rage ma sa face fatattakarsa daga karagar mulki.

KARANTA KUMA: Muhawara: Atiku, Buhari da sauran 'yan takarar Kujerar Shugaban Kasa za su fuskanci juna a ranar 19 ga watan Janairu

Kazalika Atiku ya sake jaddada matsayarsa dufufa wajen sanya Matasa da kuma Mata cikin harkokin gwamnatinsa muddin ya yi nasara a zaben 2019, inda ya ce gwamnatin za ta kunshi kaso 40 na Matasa da kuma kaso 30 cikin 100 na Mata.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar ADP, Yabagi Yusuf Sani, ya sha alwashin biyan N100, 000 mafi karancin albashin ma'aikata muddin yayi nasara a babban zabe na badi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng