A rahoton Transparency International, shin cin hanci ya ragu a karkashin Buhari ko hawa yayi?

A rahoton Transparency International, shin cin hanci ya ragu a karkashin Buhari ko hawa yayi?

- Rashawa tayi yawa a Najeriya har a wannan zamani na canji

- Buhari ya karbi mulki da burin kawo karshen ta a kasar nan

- Duk da cewa hukumar EFCC ta karbe abubuwa masu tarin yawa

A rahoton Transparency International, shin cin hanci ya ragu a karkashin Buhari ko hawa yayi?
A rahoton Transparency International, shin cin hanci ya ragu a karkashin Buhari ko hawa yayi?
Asali: UGC

A farkon shekarar nan ne hukumar Transparency International, T.I ta bayyana cewa lamarin rashawa ya tabarbare a kasar mu ta Najeriya, kuma har wannan lokaci na Buhari da APC.

Duk da cewa hukumar EFCC ta kama wadanda ake zargi sannan ta karbe dukiyoyi daga hannun shuwagabanni da yan siyasa amma har zuwa yanzu ba'a daina aikata wannan mummunar dabi'a ba.

A shekara ta 2016 kasar Kenya ta doke Najeriya a bangaren rashawa amma a halin da ake ciki yanzu tana gogawa da kasashen Afurika ta yamma inda ta koma 143 daga 145.

Duk da jajircewar shugaban kasa Muhammad Buhari akan wannan lamari wanda ya karbi mulki da kudirin kawo karshen rashawa a Najeriya.

DUBA: Me sabon littafin tsohon shugaba Jonathan da aka gabatar jiya ya qunsa?

A halin yanzu kasar Najeriya tana da matsayin 148 a bangaren rashawa inda take gogawa da Guinea da Comoros

Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel