Littafin Jonathan cike ya ke da almara da tatsuniyoyi - Gwamna Shettima

Littafin Jonathan cike ya ke da almara da tatsuniyoyi - Gwamna Shettima

- Gwamna Shettima na jihar Borno ya soki littafin da tsohon shugaban kasa Jonathan ya wallafa mai suna My Transition Hours

- Ya bayyana littafin a matsayin litaffin da ke cike da tatsuniyoyi

- Shettima ya zargin Jonathan ta yin karya game da sace 'yan matan Chibok da Boko Haram su kayi a 2014 a cikin littafinsa

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya soki littafin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya wallafa mai taken My Transition Hours sa'o'i kadan bayan kaddamar da littafin a Abuja inda ya misaltashi da tarin tatsuniyoyin yara da ke cike da almara.

Shettima ya zargi tsohon shugaban kasan da shilla karya a kan batun sace 'yan matan Sakandire na garin Chibok da mayakan kungiyar Boko Haram su kayi a shekarar 2014.

Premium Times ta ruwaito cewa batun 'yan matan Chibok din yana daga cikin abubuwan da ke kunshe a littafin.

Littafin da Jonathan ya wallafa yana cike ta tatsuniyoyi ne - Gwamnan APC
Littafin da Jonathan ya wallafa yana cike ta tatsuniyoyi ne - Gwamnan APC
Asali: UGC

Legit.ng ta gano cewar tsohon shugaban kasar ya mayar da hankali ne kan abubuwan da suka faru gabanin saukarsa a mulki a shekarar 2015 har zuwa lokacin da ya amince da shan kaye a zaben.

DUBA WANNAN: Zan biya N50,000 mafi karancin albashi - Dan takarar shugaban kasa

Jonathan kuma ya yi magana a kan abubuwan da suka rika kaiwa da komowa a yayin da akayi garkuwa da 'yan mata sama da 200 a garin Chibok da ke jihar Borno.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewar gwamnatin jihar Borno na wancan lokacin karkashin mulkin jam'iyyar APC ce da rika masa zagon kasa shi yasa ya gaza ceto yan matan na Chibok.

Ya kuma soki tsohon shugaban Amurka, Barrack Obama da gwamatinsa wadda a lokacin ya ce sun ki sayar masa da makamai da zaiyi amfani da shi wajen ceto yan matan.

A martanin da ya mayar a ranar Laraba 21 ga watan Nuwamba, Gwamna Shettima ya zargi tsohon shugaban kasan ya yunkurin yin rufa-rufa kan sakacin da gwamnatinsa tayi game da sace 'yan matan.

A sanarwan da ya fitar ta hannun mai bashi shawara a fanin kafafen yada labarai, Isa Gusau, gwamnan ya yi mamakin yadda tsohon shugaban kasan zai yi tsokaci kan batun sace yan matan Chibok tunda gwamnatinsa ba ta amince an sace matan ba ma tun farko.

Gwamnan ya ce ya karance dukkan littafin tsohon shugaban kasar a daren Talata kuma ya gano cewa almara da tatsuniyoyi ne suka cika littafin.

Ya yi ikirarin cewa Jonathan ya ki bayyana abinda kwamitin bincike da shugaban kasa ya kafa kan batun sace 'yan matan Chibok din suka gano ba inda ya zargi tsohon shugaban kasar da ragwanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel